Mu Muka Kai Buhari Villa, Amma Ya Jefa Mu Masifar Tsadar Rayuwa Inji Mawaki Rarara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu 'Rarara', ya sake zargin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da jefa ƴan Najeriya cikin masifa.
Ko a baya dai Rarara ya fito ya bayyana cewa sai da Buhari ya yi tumu-tumu da ƙasar nan kafin ya miƙa ta a hannun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A wani faifan bidiyo da wani mai amfani da sunan @bb_khamees a shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) ya sanya, mawaƙin ya zayyano illar da Buhari ya yi wa Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rarara ya bayyana cewa dole a sha wuya a Najeriya domin man da ake sayarwa a samu Dala, Buhari ya sayar da shi kafin ya sauka daga kan mulki.
Mawaƙin wanda a baya ya yi waƙokin tallata Buhari, ya ce dole ne a fito a gaya mutane gaskiya kan yadda tsohon shugaban ƙasan ya jefa ƙasar nan cikin halin ɗa ta tsinci kanta a ciki yanzu.
"Duk wannan tashin dala da wata masifa da ake ciki a Najeriya, Buhari ne ya saka mu a cikinta.
"Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda mu muka ɗauke shi muka kai shi wannan gida, muka dawo da shi muka sake kai shi, shi ya sanya mu a cikin wannan bala'in."
"Ya za a yi dala ba za ta tashi ba, dalar nan ba mu da ita, man fetur muke sayarwa a ba mu dala. Man fetur na shekara biyu daga lokacin da Tinubu ya hau, Buhari ya sayar ya karɓi kuɗaɗen. Ina za a samu dalar?"
Rarara ya yi nuni da cewa dole ne fa ƴan Najeriya su ci gaba da haƙuri domin ɓarnar da aka yi sai an sha wuya kafin a gyara ta.
A wani labarin kuma, kun ji cewa mawaƙin siyasar nan Dauda Adamu Kahutu 'Rarara', ya bayyana cewa ya cancanci samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu.
Rarara ya yi nuni da cewa gudunmawar da ya bayar wajen kafuwar gwamnatin Tinubu, ta cancanci a saka masa.
Asali: Legit.ng