Home Back

Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Mutum A Bayelsa

leadership.ng 2024/6/26
Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Mutum A Bayelsa

Wani mutum mai suna Amas ya rasa ransa sakamakon makalewa da ya yi a jikin wayar wutar lantarki a unguwar Ekeki, kusa da hedikwatar ‘yansanda da ke kan titin Azikoro a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Marigayin dai ba ma’aikacin Kamfanin Power Holding Company of Nigeria (PHCN) ba ne, amma yana zaune ne a unguwar kuma yana hada wa mutane wuta.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, sakamakon rashin wutar lantarki da ake fama da shi a jihar, akasarin mutane sun gwammace hada wutar lantarki a kan layin gwamnatin tarayya wanda ake samun wutar lantarkin akalla sa’o’i 12 zuwa 13 a kullum.

Marigayin dan asalin karamar hukumar Nembe a jihar ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu, ya makale ne a kan wayar wutar lantarkin kafin jami’an kamfanin PHCN su sauko da shi.

Wani mazaunin Azikoro mai suna Micheal Orubo wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai saukin kai wanda yake aikin hada wutar lantarki domin kula da iyalinsa.

Ya ce, “Amas yana zaune a unguwarmu, kuma yana aikin hada wuta ne a yanki. Me ya sa mutuwa za ta zo masa a haka? Ya tafi ya bar mu ba zai sake dawowa ba.

“Yana da saukin kai, wa zai kula da yaran da ya bari. Kudin da yake samu a aikin hada wutar lantarki da shi yake amfani wajen ciyar da iyalinsa. Wace irin mutuwa ce wannan? Mutumin da muke tare tsawon lokacin da ake ruwan sama yanzu, ya tafi ne da nufin idan ruwa ya dauke ya gyara musu wuta.”

Wani mazaunin yankin ya ce, “Ya wuce ni bai wuce minti biyar ba. Ruwan sama yana tsayawa, sai ihun mutane muka jiyo, nan take muka garzaya wajen da lamarin ya faru amma ba za mu iya taimakonsa ba, saboda ya daure jikinsa da bel, don haka ya makale sosai a jikin falwaya, saboda duk mun tsorata kuma har yanzu ana ruwan sama.”

Ma’aikatan kamfanin wuta na PHCN, daga baya sun zo sauke gawar daga jikin falwayar da ya makale.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Musa Muhammed bai ce komai kan faruwar lamarin ba zuwa lokacin hada wannan rahoton.

People are also reading