Home Back

MATSIN RAYUWA: Tinubu ya bada umarnin ‘yan kasuwa su yi ta jigilar shigo da shinkafa, alkama, wake, masara tsawon kwanaki 150 ba tare da sun biya harajin ko sisi ba

premiumtimesng.com 2024/10/6
TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA: Kano za ta raba buhun shinkafa lodin mota 100, dawa mota 44, gero mota 14, masara 41 a faɗin jihar

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarni ga ‘yan kasuwa cewa su fita ƙasashen waje su sayo kayan abinci, su na shigowa da shi, ba tare da sun biya ko sisin kwabo matsayin kuɗin haraji ba.

Kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin ta cire wa harajin har na tsawon kwanaki 150, sun haɗa da shinkafa, wake da irin su alkama da masara da sauran su.

Tinubu ya yi hakan ne domin a rage raɗaɗin tsadar kayan abinci da kayan masarufi, waɗanda suka addabi ‘yan Najeriya, babba da yaro.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce, “za a shafe kwanaki 180 wannan sassaucin ɗauke biyan harajin na kayan abincin da aka amince ɗin a shigo da su.”

Onanuga ya ruwaito daga bayanin Ministan Harkokin Noma, Abba Kyari, ya na cewa, “Shugaba Tinubu ya amince da janye biyan haraji kan kayan abincin da za a shigo da su, har tsawon kwanaki 150 ba tare da an biya haraji ba,” “a kan kayan abinci irin su masara, alkama da sauran su.”

Tun daga ranar da Tinubu ya cire tallafin fetur ‘yan Najeriya suka afka cikin raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da masarufi.

Sakin Najeriya a kasuwar canji domin ta neman wa kanta daraja ya ƙara karya darajar Naira, tare da tashin farashin Dalar Amurka.

Wannan lamari ya ƙara tsawwala farashin kayan abincin da ake shigowa da su da kuma nan cikin gida.

Sanarwar ta ƙara da cewa ita ma Gwamnatin Tarayya “za ta shigo da metrik tan 250,000 na alkama da metrik tan 2500,000 na masara. Alkamar da nasarar duk samfarera ne za a shigo da su, sai a bayar ga masu ƙanana da matsakaitan masana’antun casa domin su sheƙe su tare da cashewa.”

People are also reading