Home Back

Sabbin Naɗe-Naɗe 10 Da Shugaba Tinubu Ya Yi Jiya

leadership.ng 2024/8/21
Sabbin Naɗe-Naɗe 10 Da Shugaba Tinubu Ya Yi Jiya
Previous Post

Shugaba Bola Tinubu ya yi wasu muhimman naɗe-naɗen muƙamai, wanda a cewar mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai Ajuri Ngelale, sabbin naɗe-naɗen zai ƙara haɓaka ma’aikatu da kwamitocin gwamnati daban-daban.

Ga jerin sunayen waɗanda aka naɗa da mukamansu:

Mr. Silas Agara

Darakta Janar na Hukumar Samar da Aikin Yi ta Kasa (NDE)

Mr. Umar Ibrahim Mohammed

Darakta Janar na Hukumar Kula da Hidimar Ruwa ta Najeriya (NIHSA)

Baffa Dan Agundi

Darakta Janar na Cibiyar Inganta Aiki ta Ƙasa (NPC)

Cornelius Oluwasegun Adebayo

Sakataren Zartarwa/Kwamishina na Hukumar Raya Filayen Noma ta Kasa (NALDA)

Mr. Saleh Abubakar

Darakta Janar na Hukumar samar bishiyoyi kore hamada (NAGGW)

Dr. Olufemi Adekanmbi

Ko’odinetan tsaftace dagwalon iskar (HYPREP)

Mr. Tosin Adeyanju

Sakataren Zartarwa na Asusun kiyaye dokokin caca na Kasa (NLTF)

Oluwaseun Faleye

Manajan Darakta/Kwamishina na Hukumar Bada Tallafin Inshorar Jama’a ta Najeriya (NSITF)

Mrs. Mojisolaoluwa Kehinde Alli Macaulay

Daraktar Zartarwa (Harkokin Aiki) na Hukumar Bada Tallafin Inshorar Jama’a ta Najeriya (NSITF)

Ms. Omolola Bridget Oloworaran

An bada sunanta a matsayin Darakta Janar na Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom)  (Naɗin yana buƙatar amincewar Majalisar Dattawa)

Mr. Jobson Ewalefoh

An bada sunansa a matsayin Darakta Janar na Hukumar Kula da Jari-Hujja (ICRC)  (Naɗin yana buƙatar amincewar Majalisar Dattawa)

People are also reading