Annobar Kwalara Ta Yaɗu a Jihar Kano? Gaskiya Ta Fito
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ma'aikatar lafiya a Kano ta yi bayani kan halin da ake ciki a jihar bayan annobar kwalara ta bulla a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan hukuma mai kula da yaɗuwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ayyana Kano cikin jihohin da suke fama da kwalara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in yada labaran ma'aikatar lafiya ta Kano, Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana halin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai cewa annobar kwalara ba ta bulla jihar Kano ba, rahoton Daily Post.
Jami'in lafiyar ya ce a binciken da suka yi a yau Laraba ya nuna cewa babu ko mutum daya da ya kamu da kwalara a jihar Kano.
Yayin da aka tambaye jami'in lafiyar kan bayanan da hukumar NCDC ta fitar a kan bullar kwalara a Kano, sai ya ce:
'Muma haka muka ga rahoton na yawo a kafafen sadarwa amma mu a Kano bamu da mai cutar kwalara ko daya'
-Ibrahim Abdullahi, kakakin ma'aikatar lafiyar Kano
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu mutane 1,141 da suka kamu da cutar kwalara daga watan Janairu zuwa 11 ga Yuni.
NCDC ta kuma yi ikirarin cewa akwai mutane 13 da suka kamu da cutar a jihar Kano duk da cewa hukumar lafiya a jihar ta musanta ikirarin.
A wani rahoton, kun ji cewa an samu barkewar annobar kwalara a wasu kananan hukumomin jihar Legas da ke kudu maso yamman Najeriya.
Gwamnatin jihar Legas ta ce annobar ta harbi mutane da dama kuma ta jawo asarar rayuka a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar
Asali: Legit.ng