Home Back

An Gano Kudin Najeriya Da ke Asusun Kasashen Waje ya Ragu da Biliyoyin Daloli

legit.ng 2024/7/6
  • Alkaluman babban bankin kasar nan (CBN) ya bayyana cewa ana samun raguwar kudaden kasar da ke ajiye a asusun kasashen waje sosai tun daga farkon bana
  • A watan Mayu, kudin da ya rage a asusun ya ragu da $1.8bn idan aka kwatanta da watan Maris da ake da ragowar $34.44bn a asusun ajiyar wanda yake ta raguwa tun Fabarairu
  • Masana na danganta raguwar da ake samu tun daga watan Fabarairun shekarar nan da biyan basussuka da raguwar fitar da danyen man fetur zuwa kasashen waje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rahotanni sun bayyana cewa asusun ajiyar kudin Najeriya na kasar wajen ya ragu sosai a cikin makonni 10 da suka gabata.

Alkaluma daga babban bankin kasa (CBN) ya nuna cewa an samu raguwar kudin kasar nan da $1.8bn.

Bola Ahmed Tinubu
Kudin asusun kasar nan dake asusun kasar waje ya ragu da $1.8bn Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa kudin da ya rage a asusun kasar nan a ranar 29, Mayu 2024 ya kai $32.69bn, wanda ya ragu sosai idan aka kwatanta da na wata daya kafin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene ya janyo raguwar kudin kasar waje?

A watan Maris, 2024, kudin kasar nan da ke ajiye a asusun kasar waje ya kai $34.44bn, wanda ya nuna cewa an samu raguwarsa matuka.

Tun a watan Fabarairun 2023 ake samun raguwar kudin da ke asusun, kuma zuwa yanzu ya ragu da $3.4bn, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Masana sun danganta raguwar kudaden kasar nan da dalilai da dama ciki har da biyan basussukan da ake bin Najeriya.

Sauran dalilan da aka gano sun hada da raguwar fitar da man fetur kasashen ketare, raguwar zuba hannun jari daga kasashen waje da karuwar shigo da kaya cikin kasar nan.

An shawarci sanatoci kan kudin asusunsu

A baya mun kawo muku labarin cewa tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC, Timi Frank ya shawarci 'yan majalisa da su bayyana bayanan akawun dinsu na banki.

Bukatar hakan na zuwa ne bayan kalaman Godswill Akpabio da ya yi subul da baka inda ya ce an turawa 'yan majalisa kudin hutu.

Asali: Legit.ng

People are also reading