Home Back

Rikicin Masarautar Kano: Ka yi koyi da kakanka, ka hakura da sarautar Kano, Shawarar Shugaban Tijjaniyya ga Sanusi

premiumtimesng.com 2024/7/3
SARAKUNA BIYU: Yayin da jami’an tsaro na musamman daga Abuja ke gadin Sarki Bayero, ƴan farauta ke gadin Sarki Sanusi

Shugaban kungiyar Tijjaniyya, Mahi Nyass, ya shawarci Lamido Sanusi da ya yi koyi da kakansa ta hanyar kin komawa kujerar sarautar Kano.

Sarki Sanusi ne shugaban ɗarikar Tijjani ta Najeriya sannan kuma idan ba a manta ba gwamnan Kano Abba Yusuf ya maida shi sarkin Kano bayan tsige shi da gwamnatin Ganduje ta yi a baya.

Sai dai kuma gidan sarautar yanzu ta rabu gida biyu ne, Sarki Aminu Ado ya turje ba zai sauka ba, shima Sanusi ya kafe sai ya yi sarki dole.

Sai dai kuma Nyass a wata wasika da ya rubuta mai dauke da kwanan wata 3 ga Yuni, ya shawarci sarki Sanusi ya yi koyi da kakansa ya hakura da kujerar sarautar.

Mu iyalan Shaikhul Islam, Gausuzzaman, Qudwatuna ilaa Rabbina, Sheikh Ibrahim Nyass na Kaolack, Senegal, muna yin kira ga Sarki Sanusi da ya yi koyi da kakansa lokacin da aka yi masa tayin za a dawo dashi sarautar Kano bayan an tsige shi amma ya c ya hukara din a zauna lafiya.

” Shima Sarki Sanusi ya yi koyi da haka ya hakura don a zauna lafiya a jihar.

Yanzu dai maganar na kotu ana sauraren yadda za ta kaya.

People are also reading