Home Back

Tsananin Yunwa: Sarki Ya Bukaci ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashin Kayan Abinci A Yobe

leadership.ng 4 days ago
Dawanau

Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II, Ibn Umar Al-Amin Elkenemi, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da ke Jihar Yobe su taimaka wa talakawa ta hanyar rage farashin kayayyakin abinci.

Sarkin ya nuna matukar damuwarsa kan yadda farashin kayayyakin masarufi suka yi tsada sosai wanda hakan ke gagaran talaka wajen ciyar da iyalansa.

Da yake nuna rashin jin dadinsa kan yadda jama’a suke matukar shan wahala sakamakon fatara da yunwa a jihar, basaraken ya shaida wa LEADERSHIP a ranar Lahadi a masarautarsa da ke Damaturu cewa, “Akwai bukatar cikin gaggawa a yi kira ga ‘yan kasuwa da su saukaka farashin kayayyakin abinci ta yadda talakawa za su iya saya.”

Ya hori ‘yan kasuwan da su yi dukkanin mai yiyuwa wajen ganin sun zaftare farashin kayan abinci domin kishin al’umma da kuma taimaka wa masu karamin karfi da ke cikin al’umma.

A cewarsa, “Ina sanar da ku cewa, mun damu sosai kan hauhawar farashin kayayyakin abinci a jihar nan. Don haka ne nake jawo hankalin ‘yan kasuwa da su saukaka farashin kayan abinci ga jama’a, musamman talakawa da marasa karfi.”

Ya lura kan cewa tsadar kayan bukatu, musamman kayan abinci, sun jefa jama’a cikin wahala da ukuba, don haka ne ma ya janyo hankalin gwamnati da ta ci gaba da taka nata rawar wajen taimaka wa jama’an da suke cikin talauci da marasa karfi.

Ya kuma nuna wahalhalun da ake ciki da matsin tattalin arziki da talakawa ke sha a matsayin abun damuwa ga kowa, musamman wadanda sai sun fita sun yi buga-bugar neman abun da za su sanya a bakin salati su da iyalansu a Jihar Yobe da ma Nijeriya baki daya.

Basaraken gargajiyan ya kara da ba da shawara ga ‘yan kasuwa da cewa su cire dukkanin wata kumbiya-kumbiya a cikin harkokin kasuwancinsu, domin ganin an tabbatar da cewa kayan abinci sun yi sauki ta yadda talaka zai iya saya.

Kazalika, ya nemi kungiyoyi da masu hannu da suni da su fito kwansu da kwarkwatarsu su taimaki mutanen da ke fama da bukata ta musamman wato nakasassu a cikin al’umma tare da marasa karfi a irin wannan mayuwacin halin matsin rayuwa da ake ciki.

People are also reading