Home Back

ZAUNE TA TASHI TSAYE: Sojoji na farautar mutum 8 masu hannu a kisan sojoji 17 a Delta

premiumtimesng.com 2024/4/28
Sojoji sun  kashe Ƴan ta’adda 60, sun kama 50 a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya cikin makonni uku

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta fito da jerin hotuna da sunayen mutum 8 da ta bayyana cewa ta na neman su ruwa a jallo, bisa zargin su da hannu a kisan sojoji 17 a Delta.

Cikin wata sanarwa da ke ɗauke da hotunan su da sunayen su wadda Hedikwatar Tsaro ta buga a shafin ta na Facebook, a ranar Alhamis, an bayyana sunayen waɗanda ake neman da cewa sun haɗa da: Ekpekpo Arthur, wanda shi Farfesa ne, Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbo, wanda aka fi sani da Amagben da kuma Akata Malawa David.

Sai kuma Sinclear Iliki, Clement Ikolo, Reuben Baru da wata mace mai suna Ogoli Ebi.

Mummunan Laifin Da Waɗanda Ake Zargin Suka Aikata:

Yadda aka guntule kawunan sojoji 14, aka farke cikin su aka fizge zuciyar su, kuma aka guntule masu al’aura

A wani ra’ayi da PREMIUM TIMES ta buga mai ɗauke da alhini da takaicin mummunan kisan dabbancin da tsagerun Delta suka yi wa sojojin Najeriya 17, jaridar ta ce babban aikin da ke hannun jami’an tsaron Najeriya, shi ne a tabbatar da an kamo waɗanda suka yi wannan mummunan kisa, kuma a hukunta su.

Cikin bayanin da jaridar ta buga, ta bayyana cewa daga cikin sojojin 17 da aka kashe, an guntile kawunan 14, sannan aka farke cikin su aka cire zuciyar kowanen su. Kuma aka cire wa kowane azzakarin sa.

A cikin ra’ayin jaridar mai taken Munin Kisan Gillar Da Tsagerun Delta Suka Yi Wa Sojojin Najeriya, akwai kaɗan daga bayanan jaridar kamar haka:

“Babban adalcin da za a yi wa sojojin Najeriya da tsagerun Delta suka kashe, shi ne ko ta halin ƙaƙa a tabbatar da kamo makasan, kuma a hukunta su. Ta haka ne za a iya kawo ƙarshen irin wannan mummunan kisan dabbancin da aka yi wa jami’an tsaron da ke sadaukar da rayuwar su wajen kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya.

“Ɓoyayyun hujjoji sai ƙara bayyana suke yi, dangane da mummunar ranar da matsalar tsaro ta ƙazamce ƙasar nan, yayin da aka yi wa sojojin Najeriya su 17 mummunan kisan gilla, a hannun tsagerun ƙauyen Okuama cikin Jihar Delta, a ranar 14 Ga Maris.

“Ba mummunan kisa kaɗai aka yi wa sojojin ba, bayan an kashe su, an guntule kawunan 14 daga cikin su. Kuma aka farka cikin su, aka fizgo zuciyar kowanen su. Ba a nan wannan dabbanci ya tsaya ba. Sun kuma bi gawarwakin sojojin ɗaya bayan ɗaya sun guntule al’aurar su. Ƙololuwar kisan dabbanci kenan.

“Yayin da wannan bala’i ya zo daidai lokacin da masu garkuwa da kuma Boko Haram ke ƙara maƙasura, inda aka sace sama da mutum 500 na ɗalibai da masu gudun hijira a Kaduna da Barno, hakan na nuni da irin jan aikin da ke gaban manyan jami’an tsaron ƙasar nan.

“Amma kuma babban darasin da kowa zai ɗauka a wannan mummunan yanayi, shi ne, ba wanda zai iya bugun ƙirji ya ce shi dai wannan bala’i ba zai iya ritsawa da shi ba.”

 
People are also reading