Masoud Pezeshkian ya lashe zaben Iran
Masoud Pezeshkian ya samu nasarar lashe zaben kasar Iran da kuru'u miliyan 16, inda abokin karawarsa Saeed Jalili ya samu kuru'u miliyan 13 a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Juma'a.
Shugaban mai shekaru 69 da haihuwa da ke zama tsohon ministan kiwon lafiya ya yi alkawarin kawo gagarumin sauyi ga kasar a idon duniya. Sai dai duk wani buri da ake tsamannin ya zai kawo a siyasar cikin gida da ta kasashen waje, cikakken iko na zartar da komai na hannun jagoran juyin juya halin kasar Ayatullah Ali Khamenei.