Home Back

Liverpool ta dauki fansa a kan Tottenham a Premier

bbc.com 2024/5/18
Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta yi nasarar doke Tottenham da cin 4-2 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara a Anfield ranar Lahadi.

Minti na 16 da fara wasa Liverpool ta ci kwallo ta hannun Mohamed Salah, yayin da Andrew Robertson ya kara na biyu daf da za su je hutun rabin lokaci.

Kwallo na 12 kenan da Salah ya ci Tottenham a wasan da yake a Turai, Manchester United yafi zurawa kwallaye har 14 a dukkan fafatawa.

Kuma kwallo na tara da ya zura a ragar Tottenham a Premier League, ya yi kan-kan-kan da Harry Kane a wannan bajintar, wanda yanzu ya koma Bayern Munich.

Haka kuma Salah ya zama na farko a Premier League da ya ci kwallo 10 ko fiye da haka, sannan ya bayar da 10 ko fiye da haka aka zura a raga a kaka uku a jere.

Kuma Salah shi ne na biyu da yake cin kwallo 10 ko fiye da 10 a kaka biyar a Premier League, bayan bajintar Wayne Rooney.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Cody Gakpo ya kara na uku, sannan Harvey Elliott ya kara na hudu a wasan da Liverpool ta hada maki uku..

Daga baya ne Tottenham ta zare biyu ta hannun Richarlison da kuma Heung-min Son.

Wannan shi ne wasa na 300 da Son ya buga a Premier League, ya zama na uku a Tottenham mai yawan buga wasanni, bayan Hugo Lloris mai 361 da Harry Kane mai 317.

Wannan shi ne karon farko da Tottenham ta yi rashin nasara hudu a jere a Premier tun bayan shida da aka doke ta daga Oktoba zuwa Nuwambar 2004.

Tun bayan da Tottenham ta ci Nottingham Forest 3-0 a farkon makon Afirilu daga nan Newcastle ta doke ta 4-0, sai rashin nasara a hannun Arsenal 3-2 da kuma 2-0 da Chelsea ta dura mata.

Kungiyar Anfield ta dauki fansa kan Tottenham, wadda ta ci Liverpool 2-1 a wasan da ta kai takaddama, har aka bai wa Curtis Jones da Diego Jota jan kati.

Wannan shi ne wasa na 30 a bayaa da suka fuskanci juna, inda Liverpool ta ci 20 da canjaras tara, wanda Tottenham ta ci shi ne 1-0 cikin Mayun 2011.

Jurgen Klopp ya hada maki 701 a gida daga karawa 332 da ya ja ragamar Liverpool, wadda yake kaka ta tara da ita.

People are also reading