Home Back

RAHOTON MUSANMAN: Tinubu ya cire surukin Buhari daga shugabancin Kamfanin Buga Kuɗi da Muhimman Takardun Sirri

premiumtimesng.com 2024/8/22
UMARNIN TINUBU GA KWASTAM: “Ku maida wa mutane abincin su da ku ka kwace a iyakokin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya umarci a cire Shugaban Kamfanin Buga Kuɗaɗe da Takardun Sirri na Najeriya, wato Nigerian Security Printing and Minting Company Plc, (NSPM), Ahmed Halilu.

PREMIUM TIMES ta tattabar da umarnin wanda Tinubu ya bayar, na cire Ahmed Halilu, wanda surukin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ne.

Tinubu ya bayar da umarnin cire shi da kuma wasu manyan shugabannin kamfanin su huɗu daban.

Halilu dai ɗan uwa ne ga A’isha Buhari, matar Buhari. Buhari ne ya naɗa shi a cikin watan Satumba, 2022.

Sauran waɗanda korar ko saukewar ta shafa sun haɗa da Babban Darakta Ado Ɗanjuma, Babban Darakta na Legas, Chris Orewa, Babban Darakta Tunji Kazeem da Sakataren Kamfani, Victoria Iraboh.

Ita dai Victoria Iraboh matar tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa ne, Janar Lucky Irabor mai ritaya, wanda ya yi zamani da Buhari.

Idan ba a manta ba, cikin 2023 Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta kange Godwin Emefiele daga kamun da jami’an Hukumar SSS suka nemi yi masa. An danƙara sojoji a gida a ofishin Emefiele a lokacin, don kada SSS su kama shi.

A yanzu naɗa Babban Daraktan Ayyuka, Abubakar Minjibir matsayin Shugaban NSPM, sai dai ba a sani ba a san dalilin da ya sa shi ma Minjibir ɗin ba a cire shi ba.

Kakakin Babban Bankin Najeriya, Hakama Sidi, ba ta amsa kira ko maida bayanin saƙon tes da wakilin mu ya yi mata ba, domin jin ƙarin bayanin daga CBN, wanda kamfanin na buga kuɗaɗen ke ƙarƙashin sa.

Sai dai majiya daga CBN sun tabbatar wa wakilin mu cewa waɗanda aka cire ɗin an umarce su da su fice daga ofishin cikin gaggawa.

Wannan jijjiga da aka yi wa kamfanin ta zo watanni bayan rahoton Jim Obazee mai binciken badaƙalar kuɗaɗe a CBN lokacin Godwin Emefiele, ya miƙa wa Shugaba Tinubu rahoton binciken da ya sa ya yi.

Rahoton dai ya bayyana irin mummunar rawar da Kamfanin Buga Kuɗaɗe a ƙarƙashin Ahmed Halilu surukin Buhari ya taka, a harƙallar buga sabbin kuɗaɗe, lamarin da ya kusa durƙusar da Najeriya da ‘yan ƙasa baki ɗaya.

People are also reading