Home Back

Babban Bankin Sin Ya Samar Da Karin Dama Ta Lamuni Don Tallafawa Sassan Noma Da Kananan Sana’o’i

leadership.ng 2024/10/5
Babban Bankin Sin Ya Samar Da Karin Dama Ta Lamuni Don Tallafawa Sassan Noma Da Kananan Sana’o’i

Babban bankin kasar Sin ya sanar da cewa, ya kara adadin kudaden lamuni, wadanda za su bayar da damar tallafawa sassan bunkasa noma da kananan sana’o’i, a yankunan larduna 12 da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar.

A Talatar nan ne babban bankin na Sin ya sanar da hakan, inda ya ce adadin lamunin da za a kara bayarwa karkashin wannan manufa, zai karu da yuan biliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 13.99, ga sassan da suka cancanta a Chongqing, da Fujian, da Guangdong, da Guangxi, da Henan, da Heilongjiang. Sauran su ne lardunan Hunan, da Jilin, da Jiangxi, da Liaoning, da Shaanxi da Sichuan.

Manufar sake bayar da kudaden lamunin ita ce babban bankin ya tallafawa cibiyoyin hada hadar kudade da rance, kan wani adadi na kudin ruwa, da nufin daidaita adadin kudaden dake kewayawa, ta yadda za a cimma nasarar samar da moriyar manufofin bayar da lamuni. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading