Home Back

Don Allah Ku Saka Jihar Kano Cikin Addu’a, Suna So Su Kunna Mata Wutar Tashin Hankali, Daga Imam Murtadha Gusau

premiumtimesng.com 2024/7/6
Don Allah Ku Saka Jihar Kano Cikin Addu’a, Suna So Su Kunna Mata Wutar Tashin Hankali, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Muna kira ga al’ummar Najeriya, da su taimaka domin Allah, su sanya jihar Kano cikin addu’o’in su masu albarka, domin tabbas akwai yunkuri da mutanen nan suke yi na amfani da kotu gobe Juma’ah, domin su tayar da fitina a jihar.

Suna so ta ko halin kaka, suyi amfani da kotu, su murde shari’ah karfi da yaji, su nuna karfi, suyi amfani da jami’an tsaro, domin su cimma burinsu.

Dokokin tsarin mulkin kasar mu mai albarka Najeriya, sun ba wa Gwamna cikakken iko a jiharsa, na cire Sarki da kuma nada duk wanda yake so, wanda ya yarda da shi, wanda ya amince dashi, kuma yake ganin zai bashi goyon baya da hadin kai, domin suyi aiki tare, na ciyar da jihar Kano gaba, tare da taimakawa dukkanin al’ummar Kanawa.

Gwamna Ganduje yayi abun da yaga dama, bisa zalunci, ya sauke Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II, a lokacin da yake Gwamna. A lokacin Sarki Muhammad Sanusi bai yi jayayya ba, bai yi gardama ba, bai tayar da hankalin kowa ba, ya dogara ga Allah, kuma yayi kira ga dukkanin magoya bayansa da masoyansa, akan suyi hakuri, kar su tayar da hankalin kowa. Sandiyyar haka, Allah ya kalli niyyarsa da ikhlasin sa, ya dawo da shi gidan Dabo, wanda dama can shi Kanawa suke so a matsayin Sarkin su.

‘Yan majalisar jihar Kano sun yi dukkanin abunda ya dace, Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma ya amince, aka bi duk hanyar da ta dace, wadda bata saba doka ba, aka dawo da Sarki Sanusi.

To a halin yanzu sun kara shigo da jami’an tsaro cikin jihar Kano, daga wurare daban-daban, domin cimma wannan manufa tasu. Suna so ta ko wane hali, sai an cire Sarki Sanusi.

Daga cikin shirin su, akwai cewa za’a shigar da Aminu Ado gidan Sarki, ko ta wane hali, da an fita zuwa sallar Idi.

Duk wani mai hankali yana sane da cewa, mutanen nan tashin hankali da rigima kawai su ke so lallai sai ta barke a jihar Kano, daga gobe Juma’ah zuwa ranar sallah.

Sunyi amfani da duk wata hanya, da duk wata dama, sunyi kokarin shirya zanga-zanga, amma dai duk Allah ya dakile ta, saboda al’ummar jihar Kano suna son Sarkin su, Muhammad Sanusi ll.

Don haka yanzu tun da sun ga cewa duk wata hanya da suka bi babu nasara, shine suka ce to yanzu zasu yi amfani da kotu, zasu yi amfani da karfi.

Don haka kenan suna so su nuna wa duniya cewa Gwamnan jihar Kano ba ya da wani amfani, ko kuma bai isa ba.

Su babu ruwansu da bin doka, babu ruwansu da mutunci, matukar zasu cimma burinsu.

Al’amarin da ya kebanta kawai da kotun jiha, yanzu tilas, da karfi sun shigo da kotun tarayya, kawai don cimma wannan mummunar manufa tasu.

Saboda haka, don Allah muna kira da ku sa jihar Kano cikin addu’a, domin tabbas zalunci ake shirin yi, kuma so ake yi a jefa jihar Kano cikin tashin hankali.

Da ma suna jin haushin zaman lafiyar da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya albarkaci jihar da shi. Sun ga cewa irin tashe-tashen hankula da suke faruwa a wasu jihohi babu su a jihar Kano, shine suke so su tsunduma ta cikin rigima da tashin hankali a halin yanzu, kawai saboda son zuciyar su.

Al’ummar jihar Kano mutane ne masu son zaman lafiya da ci gaba. Sun shirya gagarumin hawan daba, a wannan babbar sallar mai zuwa, amma mutanen nan sai da suka bi duk wata makarkashiya, suka jawo jami’an tsaro suka soke hawan dabar.

Kuma ko sanarwar hana hawan dabar da aka yi, babu yawun gwaman a ciki. Ba’a kuma tuntube shi ba aka fitar da sanarwar an hana.

To yanzu daga cikin shirin su, akwai cewa, in dai har Aminu Ado ba zai yi Sarki ba, to Muhammad Sanusi ma ba zai yi ba. Shi yasa yanzu suke ta kokari, suke ta bin hanyoyin da duk zasu bi, domin ganin an fitar da Sarki Sanusi daga gidan Dabo.

To su sani, Allah yafi su. Kuma su sani, Sarki Muhammad Sanusi da dukkanin masoyansa, ba sa nufin kowa da sharri, sanadiyyar haka Allah yake ta yi masu fada, don haka Allah zai ci gaba da kare Sarki Sanusi da masoyansa.

Kuma irin dimbin baiwa da daukaka da daraja da Allah yayiwa Sarki Sanusi, shi yasa yake da tarin makiya masu yawa, masu yi masa hassada.

Kuma don Allah a ina ne a Najeriya aka taba yanke hukunci a kotu, kuma aka hana mutum ya daukaka kara (Appeal)? Sai a Federal High Court da take a Kano? Domin takardun hukuncin ma da suka yanke sun rike, basu ba kowa ba, saboda sun shirya wata makarkashiya.

Suna so suyi amfani da hukuncin, su fitar da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi daga gidan Sarki. Sun kawo jami’an tsaro daga jihohi daban-daban, wadanda suke fama da matsalar kidnapping, wai dole sai sun fitar da Sarki Sanusi daga Gidan Dabo.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, baya son a zubar da jinin bayin Allah, amma su abinda suke so kenan ya faru, kawai don an cire su daga Sarauta.

Don Allah wannan abun da yake faruwa a Kano, an isa a tafi wata jiha daga jihohin kudu ayi shi? To me yasa sai a Kano, sai a arewa?

Daga karshe, muna kira ga al’ummar duniya da al’ummar Najeriya baki daya, su zama shaida, akan abunda yake faruwa a jihar Kano. Kuma muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya ba jihar Kano zaman lafiya, da yankin arewa da ma Najeriya baki daya; Allah yaci gaba da kunyata makiyan jihar Kano da Kanawa, amin.

Wassalamu alaikum,

People are also reading