Home Back

Wane ne ke da haƙƙin mallakar filayen duniyar wata da sararin samaniya?

bbc.com 2024/10/6
A frantic rush to explore the moon for natural resources and glory

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Rebecca Morrell
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC

Ana yin ƴar rige-rige zuwa duniyar wata saboda a baya kasashe da kamfanoni da dama sun sanya ido kan duniyar wata domin neman albarkatun kasa da sarrafa sararin samaniya. Ko mun shiga zamanin zaƙulo albarkatun da ke duniyar wata?

Hotunan tutar China tsaye a duniyar wata sun karade duniya a wannan makon. Wannan shi ne karo na huɗu da China kuma wannan shi ne karo na farko a tarihi da tawagar bincike ta isa har ƙarshen duniyar kuma shi ne karon farko da aka kawo wasu bayanai daga can zuwa duniya.

A cikin wata 12 da suka gabata, kumbon Indiya da Japan sun sauka a duniyar wata. A watan Fabarairu, kamfanin Amurka "Intuitive Machines" ya zama kamfani mai zaman kansa na farko da ya aika mota mai ɗauko bayanai daga duniyar wata.

NASA na son mayar da mutane zuwa duniyar wata. Ƴan sama jannati na shirin zuwa duniyar wata nan da 2026. China ta ce nan da 2030 za ta tura mutanenta zuwa duniyar wata, a wani yunƙuri na samun wurin zama na din-din a can.

Sai dai sabon rikici na siyasa tsakanin manyan kasashen duniya na iya haifar da rikicin da ka iya kawo cikas ga ƙudurin na China.

"Dangantakarmu da wata zai kawo gagrumin sauyi, " In ji Justin Holcomb, masanin duniyar Earth da ke jami'ar Kansas

Ya kara da cewa: "yanayin yadda ake binciken sararin samaniya ya wuce dokokin da muka gindaya." Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1967 ta nuna cewa "babu wata kasa da ke da hakkin mallakar wata." amma yarjejeniyar mai suna 'Outer Space Treaty' ta ce kowa na da haƙƙin mallakar, kuma duk abin da za a ɗauka dole ne ya kasance abu ne da zai amfani al'umma, kuma dole sai da amincewar duka ƙasashen.

Duk da cewa yarjejeniyar tana nuna zaman lafiya da haɗin kai, ba haɗin kai ne manufarta ba, siyasa na taka rawa wajen amfani da yarjejeniyar, musamman a lokacin yaƙin cacar baka.

Ƙaruwar takun-saƙa tsakanin Amurka da tarayyar Soviet, bayan yaƙin duniya na biyu, ya haifar da fargabar cewa sararin samaniya zai koma fagen yakin soji.

Babban muhimmin bangare na yarjejeniyar shi ne hana aika makaman nukiliya zuwa sararin samaniya. Kasashe 100 ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.

Amma rige-rigen da ake na sararin samaniya a halin yanzu ya bambanta da na wancan lokacin.

Babban abin da ya bambanta shi ne ba a taƙaita aika kunbo duniyar wata ga kasashe kadai ba , har da kamfanoni masu zaman kansu.

A watan Janairu, wata tawagar masana ta Amurka mai zaman kanta ta sanar da cewa za ta dauki DNA na mutane , da abubuwan sha zuwa duniyar wata. Sai dai yoyon mai ya hana su kaiwa inda aka nufa.

Image from the far side of the moon

Asalin hoton, CHINA NATIONAL SPACE ADMINISTRATION VIA AFP

Sai dai hakan ya haifar da muhawara game da tanade-tanaden yarjejeniyar sararin samaniya, da kuma yadda irin wannan yarjejeniyar za ta yi amfani ga al'umma.

"Mun fara aika wasu abubuwa zuwa duniyar wata don kawai za mu iya yin hakan,ba tare da bin ƙa'ida kowa wani tsari ba" in ji Michelle Hanlon, lauyar sararin samaniya.

Ta ƙara da cewa " watan ya dawo wajenmu shi ya sa muka fara ɓata duniyarsa."

Duk da yadda kamfanoni masu zaman kansu ke kan gaba kan batun duniyar wata, amman har yanzu ƙasasshe na rige-rige kan hakan. Farfesa Saeed Musharr daraktan cibiyar ƙaidoji da dokokin sararin samaniya ta Birtaniya ya ce dole ne kowace ƙasa ta samu izini kafin ta iya aika wani abu zuwa sararin samaniya.

Duk da cewa duniyar wata a keɓe take, amman tana dauke da ma'adanai da suka hada da kasar da ba kasafai aka fiye samunta ba, iron, titanium, da helium, wadanda ake amfani da su wajen kera komai tun daga na'urori masu karfin gaske zuwa na'urorin asibiti da likitoci ke amfani da shi.

An yi ƙiyasin cewa albarkatun da ke duniyar wata sun zarce malala gashin tunkiya, hakan ya sanya wasu ke kallon wurin a matsayin inda za su samu kudi masu yawa, sai dai wannan wani abu ne da zai dauki lokaci.

A shekarar 1979, wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa ta bayyana cewa babu wata ƙasa ko ƙungiya da ke da haƙƙin mallakar albarkatun duniyar wata. Sai dai yarjejeniyar ba ta samu ƙarbuwa sosai ba, domin kasashe 17 ne suka shiga cikinta, ciki har da kasar Amurka da ta kai ga duniyar wata.

Amurka ta ba da wata doka a 2015 inda ta ba wa 'yan kasarta da kamfanoni damar hakowa, amfani da kuma sayar da albarkatun sararin samaniya.

Chinese lunar rover on the far side of the moon

Asalin hoton, Reuters

A cikin duniyar wata akwai ruwa daskararre da ke rufe ramukan rana.

Mutane za su iya shan ruwa, za kuma a iya samar da iskar oxygen, haka kuma ƴan sama jannati na iya amfani da ruwan wajen yin mai na jirginsu wanda zai ba su damar zuwa duniyar Mars da gaba da can.

Amurka na ƙoƙarin ganin ta samar da ƙa'idoji na bincike da gano albarkatun da ke duniyar wata.

Sama da ƙasashe arba'in ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar. Sai dai ƙasar China ba ta cikin ƙasashen da suka amince da yarjejeniyar, saboda ƙasashe da dama na ganin bai kamata wata ƙasa ce za ta sanya dokar da ta shafi duniyar wata ba.

People are also reading