Home Back

Ana Tsaka da Shari’ar Sarautar Kano, Abba Ya Biya Wa Ɗalibai 119,903 Kudin NECO

legit.ng 2024/7/2
  • Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 2.9 domin biya wa ɗalibai 119,903 kudin jarabawar NECO da NBAIS ta 2024
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin biyan kudin a wani yunkuri na tabbatar da cewa ƴaƴan talakawa sun yi karatu
  • Kwanishinan ilimi na jihar Kano, Dakta Umar Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin ganawa da manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince a fitar da Naira biliyan 2.9 domin a biya wa ƴaƴan talakawa kuɗin jarabawar NECO da NBAIS.

Akalla ɗalibai 199,903 da suka fito daga gidajen marasa galihu a faɗin jihar Kano ne za su amfana da tallafin kudin a shekarar 2024.

Gwamnatin Kano ta yi magana kan kudin NECO
Kano: Abba ya biya wa ɗalibai 119,903 kudin jarabawar NECO. Hoto: @Kyusufabba Asali: Twitter

An sanya sharaɗin biyan kuɗin jarabawar

Kwamishinan ilimi na jihar, Dakta Umar Doguwa ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin ganawa da manema labarai a Kano, in ji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Umar Doguwa ya ce za a zaɓi daliban da za a ba tallafin ne daga cikin waɗanda suka samu aƙalla makin 'C' a darusa huɗu a jarabawar 'Mock' da aka yi a kwanan baya.

Kwamishinan ilimin ya ce wannan na daga cikin kudurorin gwanatin Abba Yusuf na tabbatar da dalibai marasa galihu sun yi karatu mai zurfi.

Jajurcewar Abba kan karatun ƴaƴan talaka

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin jihar za ta biya wa kowane ɗalibi Naira 24,250 kuɗin NECO da kuma Naira 21,000 kuɗin NBAIS.

Dakta Doguwa ya ce da farko an nemi a biya wa daliban da suka samu 'C' a darusa takwas kaɗai amma Abba ya ƙi yarda.

Kwanishinan ya ce gwamnan jihar ya ba da umarnin a biya kudin jarabawar ga duk ɗalibin da ya samu 'C' a darusa huɗu domin amfanar ƴaƴan talakawa masu yawa.

An yi zaman shari'ar masarautar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke sauraron shari'ar rigimar masarautar Kano ta yi zama a ranar Alhamis tare da ɗaukar mataki.

A zaman kotun, lauyan gwamnatin jihar, Ibrahim Wangida ya shaida wa kotun cewa ba ta da hurumin sauraron wannan ƙarar, inda ya kafa misalai.

Asali: Legit.ng

People are also reading