Home Back

Fasahar Ƙirƙirar Girgije Ce Ta Jawo Ambaliyar Ruwa a Dubai? Abin da Bincike Ya Nuna

legit.ng 2024/5/7

An samu rubuce-rubuce da dama a intanet inda mutane ke iƙirarin ambaliyar ruwan sama a Dubai ta faru ne sanadin fasahar ƙirƙirar ruwan sama da ƙasar ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A shafukan Twitter, Instagram har ma da Facebook, an ga yadda mutane ke yi wa daular Larabawa (UAE) shaguɓe da cewa 'tana girbar abin da ta shuka ne.'

Amma, menene gaskiya kan wannan ikirarin na cewa fasahar ƙirƙirar ruwan sama da UAE ta yi ne ya jawo ambaliyar ruwan? Legit Hausa ta yi nazari kan hakan.

Abin da bincike ya nuna kan musabbabin ambaliyar ruwa a Dubai
Bincike ya nuna fasahar kirkirar gajimare ba da ta alaka da ambaliyar ruwa a Dubai. Hoto: @EhikhuenmenM Asali: Twitter

Amma bari mu fara duba rubuce-rubucen da ma'abota amfani da shafukan sada zumunta suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marka-markar ruwan sama a Dubai

Mu fara waiwayen ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a Dubai a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024.

Wannan marka-markar ruwan ya jawo ambaliya sosai a Dubai, inda aka yi zargin mutane 19 sun mutu a Oman, yayin da aka nemi wasu biyu aka rasa.

Tun a shekarar 1949 da Dubai ta fara adana bayanan saukar ruwan sama, masana sun ce ruwan na ranar 17 ga wata shi ne mafi yawa wanda ya jawo ambaliya, in ji rahoton CNN.

Ya fasahar ƙirƙirar ruwan sama take?

Cibiyar bincike ta Desert, a shafinta na yanar gizo ta ce ana amfani fasahar 'cloud seeding' wajen ƙirƙirar ruwan sama ko dusar ƙanƙara ko kuma takaita zubarsu.

Ana watsa wasu sinadarai a sararin samaniya da za su rikide su zama gajimare (domin yin ruwan sama) ko kuma sinadarin ƙanƙara (domin yin dusar ƙanƙara).

Sinadaran da ake amfani da su sun hada da silver iodide, potassium iodide, busassar ƙanƙara da gishiri (na musamman) - dukansu suna jawo danshin ruwa.

Fasahar 'cloud seeding' na iya jawo ambaliya?

Tambayar da kowa ke yi ita ce amfani da fasahar ƙirƙirar ruwan sama na iya jawo irin wannan ambaliyar da ta faru a Dubai?

Bisa ga rahoton kafar watsa labarai ta Emirates News Agency, Dubai na samun ruwan sama mai zurfin 59.73 a shekara, idan yana zubar 2.5 zuwa 7.5mm a kowacce awa.

Sai dai ruwan da aka yi a ranar 17 ga wata ya haura zurfin 145mm, wanda masani a jami'ar Reading, Maarten Ambaum ya ce Dubai ba ta da fasahar iya ƙirƙirar ruwa mai wannan karfin.

Ambaum ya ce a zahirin gaskiya ma kasar Dubai ba ta yi amfani da fasahar ƙirƙirar ruwan sama a 'yan kwanakin nan ba balle ace shi ne silar mamakon ruwan.

Neman tabbaci kan ikirarin Mr Ambaum

Jaridar The Cable ta tuntubi Taiwo Ogunwumi, masanin ambaliyar ruwa a cibiyar Geohazard Risk Mapping, kan abin da ka iya jawo irin wannan ambaliyar ruwan ta Dubai.

Ogunwunmi ya ce hayaki mai gurbata muhalli daga ayyukan jama'a na iya zama sanadin afkuwar wannan ruwan saman na Dubai.

Ya ce duk da fasahar 'cloud seeding' na iya jawo ambaliya amma ba za a iya alakanta fasahar da jawo ambaliyar ba tunda masana sun hakaito za ayi ruwa a wannan ranar.

Haka ita ma Gloria Okafor, lakcara a jami'ar Nigerian Maritime da ke Delta, ta ce ruwan da aka tafka a Dubai ya fi karfin fasahar ƙirƙirar ruwan sama.

Okafor ta ce ruwan saman ba zai rasa nasaba da hasashen masana kimiyya na cewar duniya na dab da shiga ƙarnin 'El Nino' wanda ke faruwa duk bayan shekaru bakwai, kuma ana yin watanni 12 a cikinsa.

Abin da bincike ya nuna

Bisa ga dukkanin bincike da kuma tambihin masana kimiyyar ruwan sama da ambaliya, ƙarshen wannan bincike ya nuna cewa:

  • Babu kwakkwarar hujja na cewa fasahar ƙirƙirar ruwan sama ce ta jawo ambaliya a Dubai
  • Mamakon ruwan sama a Dubai ba daga fasahar 'cloud seeding' bane tunda an yi hasashen ruwa a ranar
  • Dubai ba ta karfin fasahar ƙirƙirar ruwan sama da zai iya jawo zubar mamakon ruwa haka

Abubuwan da ka iya jawo ambaliyar

Fitar hayaki mai gurbata muhalli sakamakon ayyukan jama'a.

Duniya na shirin shiga ƙarnin 'El Nino' wanda ke gudana na akalla watanni 12

Mutane 3 sun mutu a ambaliyar ruwa

A nan gida Najeriya, Legit Hausa ta ruwaito yadda mutane uku suka gamu da ajalinsu a wata ambaliyar ruwa da ta afku a Dakingari da ke karamar hukumar Sulu, jihar Kebbi.

Shugaban ƙaramar hukumar Sulu Alhaji Muhammad Lawal Suru ne ya bayyana hakan inda ya nuna damuwa kan barnar da ambaliyar ke yi a yankunansu.

Asali: Legit.ng

People are also reading