Home Back

Karancin Fetur: Kano da Wasu Jihohi na Fuskantar Dogayen Layin Mai

legit.ng 2024/5/5
  • An wayi garin Alhamis da ganin dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja
  • Rashin samun man ya kara ta'azzara farashin ababen hawa yayin da wasu gidajen man su ka ku budewa ballantana su sayarwa masu bukata man fetur
  • Sakataren kungiyar masu kasuwancin man fetur ta kasa (IPMAN), John Kekeocha ya ce za su zauna da kamfanin mai na NNPCL domin gano bakin matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-An wayi garin Alhamis da ganin dogayen layi a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Nassarawa, Niger, Sokoto, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.

Wasu gidajen man kuma sun kasance a rufe, yayin da masu ababen hawa ke ta fafutukar samun mai domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Wani rahoton da Punch News ta ruwaito ya bayyana cewa mutane da dama suna takawa saboda rashin ababen hawan da ke can su na bin layin mai.

Wasu daga gidajen man da ake sayar da fetur da dan tsada na naira dari 800 ba su da dogon layin wuraren da ake sayarwa a kan naira 620.

Masu ababen hawa na jimawa a layi

Adamu Musa Kankarofi, wani mai adaidata sahu ne a jihar Kano, kuma ya bayyanawa Legit Hausa yadda ya dade a layi kafin samun mai a gidan mai na NNPCL da ke titin Ibrahim Taiwo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun wurin 8.00 na safe ya hau layi, kuma ya samu shan mai da misalin karfe 11.00 a kan naira 620 kowace lita.

A jihar Gombe, masu ababen hawa na bin layi na tsawon awa 2, kuma sun sayi mai a kan naira 755 kowace lita.

Duk da karin farashi a wasu gidajen mai, zagayen da Legit Hausa ya yi ya gano wasu gidajen mai a Kano sun rufe.

Rahoton Punch News ya bayyana cewa an rufe gidajen mai da dama a Zuba, da ke jihar Neja, da wasu da ke titin Arab a Kubwa, Abuja.

“Za mu tattauna da NNPCL,” John Kekeocha

Sakataren masu kasuwancin man fetur na kasa (IPMAN), Cif John Kekeocha ya bayyana cewa ba su san dalilan karancin man fetur din da ake fuskanta a wasu sassan kasar nan ba.

Sai dai ya ce akwai karancin man fetur a kasar, kuma a yau za su duba batun da kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) domin shawo kan matsalar.

“Karancin man fetur zai kau,” Kyari

kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabbatarwa 'yan kasar nan cewa, nan gaba kadan zai magance karancin man fetur a Najeriya.

Babban Babban jami'in gudanarwa na kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana haka sai dai ba zai bayar da tabbacin yankewar karancin mai.

Asali: Legit.ng

People are also reading