Home Back

Kenya: Zanga-zanga ta tilasta wa gwamnati cin tuwon fashi

dw.com 2024/7/3
Hoto: LUIS TATO/AFP/Getty Images

 Wani daftarin kudirin kudade ne dai na samar da kudaden shiga ga gwamnati ya haifar da wannan gagarumar zanga-zangar a titunan Nairobi da sauran birane a wannan makon. Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu matasa ne sun yi dandazo a kofar majalisar dokokin Kenya a wannan makon. Suna ikrarin cewa karin harajin zai ta'azzara tsadar rayuwa a kasar. 'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan dandazon yan zanga zangar tare da kama wasu daruruwa. Matasan na zamani masu karfin hali da ake yi wa lakabi Generation Z ko kuma Gen Z a takaice, kalmar da ake amfani da ita wajen baiyana mutanen da aka haifa a tsakanin shekaru 1990 da kuma farkon shekarun 2000 sun nuna fushinsu kan yadda gwamnatin Kenya ke lafta dukkan matsalolinta akan yan kasa. Makena Kahuha wani dan wasan kwaikwayo ya yi tsokaci da cewa oton...... "Ta ce da ma muna biyan haraji amma ba abin da suke yi mana sai sata kawai a saboda haka yaya za mu yarda da su su yi  mana kari?

Wata 'yar zanga-zangar Pamela Mariuki ita ma ta nuna bacin ranta:"Ta ce sun fi son a yi musu biyayya a bi su sau da kafa maimakon biyan muradun mutanen da suka zabe su.Sabanin zanga-zangar baya da 'yan jam'iyyar adawa suka jagoranta, wannan karon matasa ne suka shirya zanga-zangar inda suke rera wakokin kin jinin gwamnati suna daga kwalaye da aka yi rubutu da ke yin Allah wadai da kudirin. Matasan wadanda suka rika yin artabu da 'yan sanda sun rika daukar hotuna da wayoyinsu na hannu suna yadawa a Internet da sauran kafofin sada zumunta karkashin maudu'in da suka yi wa lakabi da  OccupyParliament. wato zaman dirsham a majalisar dokoki. Kwalliya dai ta biya kudun sabulu, saboda gwamnatin ta sanar da cewa ta soke sassa da dama na daftarin kudirin mai sarkakakiya ciki har da haraji kan burodi da kuma na mallakar mota. Haka kuma gwamnatin ta ce ba za a yi kari ba kan harajin tura kudi ta waya. Gwamnatin wadda ke fama da rashin kudi da farko ta kare hujjar yin karin harajin da cewa ya zama dole domin rage dogaro a kan ranto kudi daga waje. An dai kiyasta cewa karin harajin zai samar wa gwamnatin biliyan 346 na kudin kasar kwatankwacin dala biliyan 2.7 daidai da kashi 1.9 cikin dari na dukiyar da kasar ke   samu a shekara.

Tun lokacin annobar Corona kasar ke fama da matsaloli na tsuke bakin aljihu da kuma tsadar rayuwa. Manazarta sun yi gargadin cewa halin da ake ciki zai kara tabarbarewa idan aka aiwatar da karin da gwamnatin ta sanya a daftarin kasafin da ta gabatar wa majalisar dokoki. A hannu guda dai asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bukaci gwamnatin ta kara habaka hanyoyin kudin shiga a kasafinta na 2024/2025 domin   rage ciwo bashi.

People are also reading