Home Back

Tambuwal: Tsohon Gwamna Ya Gargadi Tinubu Kan Sukar Gwamnatin Buhari

legit.ng 2024/7/5
  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsawatarwa ministocinsa kan sukar gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa Tinubu ba shi da hujjar kokawa kan halin da ya samu ƙasar nan saboda ya ci gajiyar mulkin Buhari
  • Ya yi kira shugaban ƙasan da ya mayar da hankali wajen kare al'umma, kawo ci gaba da samar da haɗin kai idan har da gaske yake kan mulkin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ja kunnen ministocinsa da waɗanda ya naɗa muƙamai kan sukar magabacinsa, Muhammadu Buhari.

Tambuwal ya bayar da hujjar cewa Tinubu ba zai iya raba kansa da gazawar gwamnatin Buhari ba, don haka ya kamata ya daina kukan ya gaji tattalin arziƙin da ya taɓarɓare.

Tambuwal ya gargadi Tinubu
Tambuwal ya bukaci Tinubu ya ja kunnen ministocinsa kan sukar Buhari Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Sokoto wanda shine Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tambuwal ya ce kan Tinubu?

Tambuwal ya bayyana cewa Tinubu ya amfana da mulkin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, rahoton jaridar The Sun tabbatar.

"Wannan gwamnatin Tinubu da ta gaza kare ƴan Najeriya ko kawo ci gaba, ita ce yanzu take kokawa sannan tana raba kanta da gazawar gwamnatin Buhari."
"Babu dalilin da zai sanya Shugaba Bola Tinubu zai bari hadimansa ko ministocinsa su riƙa sukar gwamnatin APC ƙarƙashin Muhammadu Buhari, wacce ya ci gajiyarta a matsayinsa na ɗan APC."
"Shugaba Tinubu ya kamata ya fuskanci mulkin Najeriya da idon basira sannan kada ya bari wasu bara gurbi a gwamnatinsa su lalata shirinsa na kare al'umma da kawo ci gaba da haɗin kai a ƙasarmu idan har da gaske yake yi."

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya faɗi kuskuren ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba su ɗauki shawarar da aka ba su ba a zaɓen 2023.

Tambuwal ya ce kuskuren sake zaɓen jam'iyya% APC da ƴan Najeriya suka yi ne ya jefa su ckin halin ƙuncin rayuwar da suke ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

People are also reading