Home Back

Ganduje Ya Kaddamar da Titin ‘Abdullahi Ganduje’ a Jihar Gombe

legit.ng 2024/5/7
  • Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ta kaddamar da titi mai sunan Ganduje a jihar
  • Shugaban jam'iyyar APC ta kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin kaddamar da titin da kansa
  • Ya kuma mika godiya ga gwamnatin jihar bisa karrama shi da ta yi tare da kira ga al'ummar jihar da su cigaba da goyon bayan gwamnatin.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe - Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da titin da aka sanya wa sunan sa a jihar Gombe.

Ganduje road
Gwamnatin jihar Gombe ta kaddamar da hanya mai sunan Ganduje. Hoto: Isma'ila Uba Misilli Asali: Facebook

Yayin da shugaban jam'iyyar ya ziyarci jihar Gombe domin ayyukan da suka shafi zaben kananan hukumomi, gwamna jihar ya karrama shi da sanya wa titi sunan sa.

Yadda titin yake

Cikin sanarwar da mai taimakawa gwamnan Gombe a kan yada labarai Isma'ila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook, ya nuna cewa titin mai tsawon kilomita 1.6 ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma kara da bayyana cewa hanyar ta haɗa wurare masu muhimmanci a cikin karamar hukumar Gombe da karamar hukumar Akko.

Wuraren da hanyar ta haɗa ya kunshi GRA, Nayinawa, Bagadaza, Kuwait da hanyar ratse ta bayan gari wanda dukkan su wurare ne da ake hada-hada.

Ganduje ya yi godiya

Yayin da yake kaddamar da titin, Dakta Ganduje ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa ayyukan cigaba da yake kawowa jihar.

Ya kuma kara nuna godiya ga gwamnan bisa karrama shi da yayi da sanya wa titin sunan sa tare da kira ga al'ummar jihar da su cigaba da goyon bayan gwamnan.

Shugaban jam'iyyar ya kuma aike sakon shugaba Tinubu ga gwamnan inda ya ce lalle shugaban kasan yana jin labarin yadda gwamnatin jihar ke ayyukan cigaba kuma yana alfahari da hakan.

APC ta goyi bayan Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun kaɗa kuri'ar amincewa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa

Sun tabbatar da wannan matsaya ne yayin da suka ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Talata

Asali: Legit.ng

People are also reading