Home Back

Da Arewa na samun irin Nuhu Ribaɗu kusa da shugabanni da matsalar tsaro bai addabi yankin ba

premiumtimesng.com 2024/5/19
Tinubu shugaba ne mai gaggauta ɗaukar matakan gaggawa – Nuhu Ribadu

Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu ya yi kururuwar abubuwan da suka wajaba a yi domin magance wannan gagarimar matsalar tsaro a musamman yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Ba sau da dama tun bayan naɗa shi mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da kan su ƴan Najeriya sun ga canji irin wanda basu gani a baya ba musamman wajen yaki da ta’addanci da kuma garkuwa da mutane da ya ƙi ci yaki cinyewa a musamman Arewa.

Abin farin ciki shine tun farko shi dama ba mutun ne mai burin tara abin duniya ba, talakawa da gyaran kasa shine ya fi mai da hankali a kai.

Tabbacin hakan kuwa na gaba ga kowa ya gani, irin namijin kokarin da ya yi lokacin da ya kafa hukumar EFCC da irin rawar ganin da hukumar ta taka ƙarƙashin sa.

A wasu jawabansa da ya yi a tarukka da dama a Ribaɗu ya rika bada shawarwari wajen zakulo hanyoyin da za kawo karshen matsalolin tsaro a kasar nan.

Ribadu ya bayyana matsalar tsaro a Arewa cewa “murɗaɗɗen al’amari ne wanda ke harɗe da matsalar zamantakewa da matsalar tallalin arziki da kuma matsalar ƙabilannci da batutuwa na addini.

Sannan kuma ya yi ƙarin bayani cewa irin matakan gaggawa da Shugaba Tinubu ke ɗauka wajen magance matsalolin tsaro su na haifar da ɗa mai ido sosai.

Yanzu ko a kasar nan, babu wanda bai shaida ba cewa cikin wata 11 da rantsar da wannan gwamnati ana samun nasarorin gaske wajen dakile ta’addanci da safarar muggan makamai a fadin kasar nan.

Mashawarcin ya ce “Yaƙi da matsalolin tsaro abu ne da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da sauran tsare-tsaren magance matsalolin da suka shafi fatara da talauci, rashin aikin yi, kawo ƙarshen ware wasu ba’arin ɓangarorin al’umma ta hanyar jawo su a jika, daƙile yawan tashe-tashen hankulan ƙabilanci ta hanyar ɗarsasa zaman lumana da yalwar arziki a Arewacin Najeriya.

Da irin wannan hali na shi ne da kuma kokari da kwarewa a aikin samar da tsaro da bankaɗo harkallar cin hanci da rashawa da kuma bada shawarwari domin dawo da zaman lafiya a kasar nan.

People are also reading