Home Back

‘Yansanda Sun Cafke ‘Yammata Masu Yawon Dare A Yamai

leadership.ng 2024/4/29
‘Yansanda Sun Cafke ‘Yammata Masu Yawon Dare A Yamai

A Jamhuriyar Nijar, ‘yansandar kasar sun kaddamar da wani samame na ba sani ba sabo kan mata da ‘yammata masu yawon dare.

Ofishin hukumar ‘yansanda da ke ba da kariya ga mata da kananan yara karkashin jagorancin kwamishiniya Zouera Hassan Hausaize ne ya kaddamar samamen a kan titunan Yamai.

Hukumar ta ce ta kama tarin ‘yammata masu zaman kansu da ke tsayuwa a tituna da wasu wuraren shakatawa a birnin.

Inda ta koka kan yadda ‘yammatan ke bijire wa iyayensu. Ko da yake a cewar shugabar hukumar suna samun wadanda ke yin nadama bisa hakan.

“Mun kama yara mata akan fitar dare suna bin tituna suna neman maza – Idan mun kama su muka kwo su wajenmu muna yi musu fada mu ja musu kunne, mu nuna musu cewa wannan ba wurin zuwan yaro ba ne, idan ba za su yi karatu ba to su nemi sana’ar hannu.” in ji ta

Shugabar ta kuma bayyana cewa: “Iyaye ke zuwa da kukansu su ne cewa ‘ya’yansu ba sa gane musu”

Wasu iya ye a birnin na Yamai sun koka kan yadda yara masu karancin shekaru ke shiga wannan rayuwa ta yawon banza.

Hukumar ‘yansanda na shirya irin wannan aiki lokaci-lokaci a tsarinta na yaki da miyagun dabi’u.