Home Back

“A Gwada Matasa Kawai”: Tsohon Shugaban Kasa Ya Koka Kan Shugabancinsu

legit.ng 2024/7/3
  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasano ya nemo mafita ga rashin shugabanci da ake fama da shi a kasar
  • Obasanjo ya ce a yanzu lokaci ya yi da ya kamata a ba matasa sabbin jini dama domin samar da shugabanci mai inganci
  • Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a Lagos inda ya ce Najeriya ta dawo mafi hatsarin wurin zama yanzu a fadin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya koka kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya.

Obasanjo ya ce a yanzu kasar na bukatar sabbin jini domin ci gaba da gudanar da mulkin kasar tare da kawo sauyi a Najeriya.

Obasanjo ya bukaci kawo sabbin jini a shugabannin Najeriya
Olusegun Obasanjo ya ce dole a ba sabbin jini dama a mulkin Najeriya. Hoto: @officialABAT. Asali: Twitter

Obasanjo ya bukaci ba matasa dama

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka a jiya Asabar 1 ga watan Yuni yayin wani babban taro a jihar Lagos, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rashin tsaro ya gigita kasar tare da mayar da ita mafi hatsari da mutum zai yi rayuwa a cikinta bayan yunwa da matsin rayuwa, Punch ta tattaro.

“Zan ba da hanyoyi biyu kacal, dole mu tashi tsaye wurin kyankyasar sabbin jini da za su shugabanci kasar nan gaba.”
“Shugabanni masu tarbiya da kwarewa wadanda suka dauki mulii bautar jama’a ba bautar kansu ba.”
“A yadda Najeriya take a yanzu, kowa yana cikin hatsari ba za ka iya hasashen abin da zai faru a gobe ba.”

- OLusegun Obasanjo

Obasanjo ya bayyana illar rashin shugabanci

Obasanjo ya ce Najeriya tana da arzikin kasa wanda wasu kasashe kamar Japan da Singapore ba su da shi.

Sai dai ya ce duk tarun arziki da kasa ke da shi idan har babu shugabanci to babu inda wannan arziki zai yi amfani ga kasar.

Obasanjo ya shawarci Tinubu kan tattalin arziki

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya kawo karshen matsalar tattalin arziki.

Obasanjo ya ce idan har ya gagara shawo kan matsalar zai iya tuntubar Zimbabwe da suka taba shiga irin wannan hali domin samun mafita.

Asali: Legit.ng

People are also reading