Home Back

El-Rufai Ya Yi Magana Kan Binciken da Ake Masa, Ya Fadi Makomar Uba Sani

legit.ng 2024/7/3
  • Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yi hasashen faɗuwar gwamnatin Gwamna Uba Sani wanda ya gaje shi
  • El-Rufai ya buƙaci magoya bayansa da su marawa gwamnatin Uba Sani baya da addu’a, kuma kada su damu da matakin da aka ɗauka na bincike a kan gwamnatinsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa matakin da majalisar jihar ta ɗauka na bincikar gwamnatinsa bai dame shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce bai damu da yunƙurin da majalisar dokokin jihar ke yi na bincikar gwamnatinsa ba.

El-Rufai ya yi nuni da cewa mai yiwuwa gwamnatin ba za ta yi nasara ba.

El-Rufai ya magantu kan bincikensa a Kaduna
El Rufai ya yi hasashen makomar Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan a wani taron Sallah da ya yi da muƙarrabansa a ranar Talata 18 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me El-Rufai ya ce kan Uba Sani?

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, El-Rufai ya kuma shawarce su da su guji yin cacar baki da hadiman gwamnan, inda ya yi hasashen cewa Uba Sani bayan ya gama ƴan tsalle-tsallensa, zai faɗo kamar alewa a hannun yaro.

"Ku tallafawa gwamna da ƴan majalisarsa da addu’o’i domin su yi abin da ya dace."
"Kada ku ji zafi kan abin da ke faruwa. Idan ya gama ƴan tsalle-tsallen, zai faɗo kamar alewa (a hannun yaro)."

Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan ya yi magana a bainar jama'a tun bayan da rikici ya ɓarke tsakaninsa da magajinsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading