Home Back

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Jawabin Tinubu ga 'Yan Majalisun Tarayya

legit.ng 2024/7/3

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga majalisun tarayya guda biyu a ranar Laraba.

Rahotannin dai sun ce shugaban ƙasan zai yi jawabi ne ga majalisun biyu a tare domin murnar cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta yi magana kan batun jawabin Tinubu ga majalisun tarayya
Fadar Shugaban kasa ta ce Tinubu ba zai yi jawabi ba ga taron 'yan majalisun tarayya a ranar 29 ga watan Mayu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale ne ya musanta rahotannin jawabin shugaban ƙasan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

A cikin sanarwar, Ajuri Ngelale ya bayyana cewa batun jawabin shugaban ƙasan ga majalisun guda biyu a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ƙarya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duba da bayanan da ake yi dangane da shugaban ƙasa zai yi jawabi ga zaman majalisun tarayya na tare a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun 2024, yana da muhimmanci a bayyana cewa wannan bayanin ƙarya ne.
Kuma ba a amince da hakan ba. Ofishin shugaban ƙasa ba shi hannu a wajen shirya taron"

- Ajuri Ngelale

Idan ba a manta ba dai mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar Talata ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi jawabi ga ƴan ƙasa ba a ranar Laraba domin murnar cikarsa shekara ɗaya kan mulki.

A maimakon hakan, Onanuga ya ce Tinubu zai yi jawabi ga taron majalisun tarayyar domin tunawa da cika shekara 25 da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sai dai, mai magana da yawun shugaban ƙasan ya ƙaryata hakan.

Asali: Legit.ng

People are also reading