Home Back

BIDIYO: Yadda Sasakawa ke amfani da Shirin Inganta Noma na Kano (KSADP), wajen wadatar abinci a Jihar

premiumtimesng.com 2024/4/30
BIDIYO: Yadda Sasakawa ke amfani da Shirin Inganta Noma na Kano (KSADP), wajen  wadatar abinci a Jihar

Sama da shekaru uku kenan jami’an ƙungiyar Bunƙasa Noma a Afrika, ta ƙasar Japan, wadda aka fi sani da Sasakawa Africa Association (SAA), ta kasance a sahun gaba wajen ingantawa da bunƙasa rayuwar manoma.

Sasakawa na gudanar da wannan gagarumin shiri ta hanyar amfani da lamunin Dala miliyan 19.3 da aka karɓa daga Bankin Musulunci (Islamic Development Bank), domin bunƙasa noma ta hanyar sauƙaƙa wa manoma amfani da dabarun noma domin inganta rayuwar su da kuma samar da wadatar abinci a faɗin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, a cikin shekaru biyar.

A ƙarƙashin wannan shiri, ana koyawa tare da zaburas da manoma hanyoyin noman da suka dace ta hanyar amfani da kayan noma na zamani, bada horon dabarun noma ga mata manoma domin inganta dabarun sarrafa shinkafa.Ana yin hakan ne kuwa domin rage yawan asarar da suke yi bayan girbe amfanin gonar su, tare kuma da taimaka masu yadda yadda za su riƙa ririta tattalin arzikin su.

 
People are also reading