Home Back

SHIRIN LAMUNIN ƊALIBAN MANYAN MAKARANTU: Tinubu muke jira ya amince da ranar ƙaddamarwa – NELFUND

premiumtimesng.com 2024/4/29
UMARNIN TINUBU GA KWASTAM: “Ku maida wa mutane abincin su da ku ka kwace a iyakokin Najeriya

Gidauniyar Lamunin Ɗaliban Manyan Makarantu ta Najeriya (NELFUND), ta bayyana dalilin da ya sa ta ɗage ƙaddamar da fara bayar da ramcen kuɗaɗen rage raɗaɗin tsadar rayuwa da Gwamnatin Tarayya ta shirya fara biya a yau Alhamis, 14 ga Maris.

Shugaban Gidauniyar, Akintunde Sawyer ne ya bayyana cewa ba a ɗage shirin bayar da ramcen ba sai yadda hali ya yi, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito a ranar Laraba ba.

A cikin wata ganawa da aka yi da Sawyer s Gidan Talabijin na Arise, a ranar Talata, ya ce har yanzu ana jiran ranar da Shugaban Ƙasa ya amince a ƙaddamar da shirin ne.

Ya ce duk wani shirin da za a yi, to an yi shi an gama, amincewar ranar ƙaddamawa daga Shugaba Bola Tinubu kaɗai ake jira, sai a fara.

Da farko dai an shirya ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis, 14 ga Maris, to amma sai Sawyer ya sauya magana, ya ce za a bayyana wata ranar da za a ƙaddamar da shirin nan gaba ba da daɗewa ba.

Cikin wata sanarwar da Nasir Ayitogo ya sa wa hannu a madadin NELFUND a ranar Laraba, ya ce kafafen yaɗa labarai ba su buga abin da Sawyer ya furta daidai ba.

Ya ce NELFUND za ta ƙaddamar da manhajar rajista, tunda tuni Shugaba Bola Tinubu ya amince a fara shirin.

 
People are also reading