Home Back

Sallah: Bayan Dikko Radda Na Katsina, Gwamnan Sokoto Ya Yi Abin Alkairi ga Ma'aikata

legit.ng 2024/10/5
  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah babba, ma'aikatan jihar Sokoto za su samu sauki bayan alfarmar gwamna
  • Gwamna Ahmed Aliyu na jihar ya amince da biyan albashin ma'aikata na watan Yuni daga gobe Litinin 10 ga watan Yuni
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Katsina ya ba ma'aikata kyautar N15,000 da kuma bashin N30,0000 saboda bikin sallah

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da biyan ma'aikata albashin watan Yuni daga gobe Litinin 10 ga watan Yuni.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin ragewa ma'aikata radadi da kuma yin Sallah cikin walwala.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Abubakar Bawa ya fitar a yau Lahadi 9 ga watan Yuni, cewar Tribune.

Bawa ya ce biyan zai shafi duka ma'aikatan jihar da na kananan hukumomi da kuma ƴan fansho.

Daga bisani gwamnan ya taya al'ummar Musulmai murnan shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan na biyan albashi ranar 20 zuwa 21 ga kowane wata bayan hawa karagar mulkin jihar.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading