Home Back

NAF Ta Yi Barin Wuta A Maɓoyar ‘Yan Ta’adda Da Ke Neja

leadership.ng 2024/5/19
NAF Ta Yi Barin Wuta A Maɓoyar ‘Yan Ta’adda Da Ke Neja

Rundunar sojin saman Nijeriya, NAF da ke yaki da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya sun tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda a Chinene, kusa da tsaunin Mandara da Allawa, da ke kusa da Shiroro a Jihar Neja.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya ce, rundunar sojin sama a Chinene ta lura da yadda ‘yan ta’addan ke taruwa domin wani taro a wani wuri da ke cikin yankin tsaunin Mandara a ranar 3 ga Mayu, 2024.

AVM Gabkwet ya ce, an ga ‘yan ta’addan suna taruwa, watakila domin wani taro da manyan motoci 7 masu dauke da bindiga da ake kafewa, an boye motocin a karkashin bishiyoyi.

“Bayan kai harin, rahoton na’ura mai kwakalwa, ya bayyana cewa, an yi nasarar kai hare-haren domin an kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da lalata makamansu da maboyarsu,” in ji shi.

People are also reading