Home Back

An Kashe Matashi Yayin da Yake Ƙoƙarin Tallata Sabon Addini a Wata Jihar Arewa

legit.ng 2024/7/1
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa a kauyen Nasaru da ke jihar Bauchi sun halaka wani matashi a ranar Laraba
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an kashe matashin mai suna Yunusa Usman a lokacin da yake tallata sabon addini
  • Majiyoyi na zargin cewa wasu matasa ne suka yi wa Yunusa Usman dukan tsiya har ya mutu saboda kalaman batanci ga Annabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da wani mummunan lamari da ya faru a kauyen Nasaru a ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi.

A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Bauchi, Ahmed Wakili, wani matashi mai suna Yunusa Usman ne aka kashe saboda tallata sabon addini.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan matashin da aka kashe a Bauchi
An kashe matashi mai tallata sabon Addini a jihar Bauchi. Hoto: Legit.ng Asali: Twitter

An kashe matashi mai tallar addini

Ahmed Wakili ya bayyana cewa matashin ya fara yi wa mazauna kauyen da'awar addinin 'Fera Movement', lamarin da ya harzuka su, suka kashe shi, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Muhammad, ya yi kakkausar suka ga abin da masu hannu a kisan matashin suka aikata, inda ya jaddada muhimmancin bin doka da oda.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin kara sanya ido a yankin domin tabbatar da tsaro da kuma ganin cewa wannan lamarin bai haifar da tashin tarzoma ba.

Ana zargin Yunusa da kalaman batanci

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa ne suka yi wa marigayi Yunusa Usman dukan tsiya har ya mutu saboda furta kalaman batanci.

An zargi Yunusa da furta kalaman batanci a kan Annabi Muhammad (S.A.W). Wani ganau daga kauyen Nasaru ya yi ikirarin cewa:

"Wasu samari sun nemi Yunusa da ya janye kalamansa, amma ya ki yin hakan. Har ma ya nanata kalaman nasa. A lokacin ne suka fara dukansa.”

An halaka mai batanci a Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

Asali: Legit.ng

People are also reading