An Kashe Matashi Yayin da Yake Ƙoƙarin Tallata Sabon Addini a Wata Jihar Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da wani mummunan lamari da ya faru a kauyen Nasaru a ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Bauchi, Ahmed Wakili, wani matashi mai suna Yunusa Usman ne aka kashe saboda tallata sabon addini.
Ahmed Wakili ya bayyana cewa matashin ya fara yi wa mazauna kauyen da'awar addinin 'Fera Movement', lamarin da ya harzuka su, suka kashe shi, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Muhammad, ya yi kakkausar suka ga abin da masu hannu a kisan matashin suka aikata, inda ya jaddada muhimmancin bin doka da oda.
Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin kara sanya ido a yankin domin tabbatar da tsaro da kuma ganin cewa wannan lamarin bai haifar da tashin tarzoma ba.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa ne suka yi wa marigayi Yunusa Usman dukan tsiya har ya mutu saboda furta kalaman batanci.
An zargi Yunusa da furta kalaman batanci a kan Annabi Muhammad (S.A.W). Wani ganau daga kauyen Nasaru ya yi ikirarin cewa:
"Wasu samari sun nemi Yunusa da ya janye kalamansa, amma ya ki yin hakan. Har ma ya nanata kalaman nasa. A lokacin ne suka fara dukansa.”
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Asali: Legit.ng