Home Back

GAYYATAR GUMI OFISHIN JAMI’AN TSARO: ‘Sun girmama ni, mun tattauna hanyoyin da za a magance matsalar ‘yan bindiga

premiumtimesng.com 2024/4/30
Jigon APC ya nemi hukumomin tsaro su kama Sheikh Gumi kan kalaman da ya yi ga Wike

Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheik Ahmad Gumi, ta bayyana cewa sun yi tattaunawar fahimtar juna shi da jami’an tsaron Najeriya, waɗanda suka gayyace shi dangane da batutuwan matsalolin tsaro.

Bayan amsa gayyatar da Gumi ya yi a ranar Litinin, ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa shi fa bai fi ƙarfin doka ba, wanda bai aikata laifi ba shi ne bai fi ƙarfin doka ba.

Ya ce babu wani abin tayar da hankali dangane da gayyatar jami’an tsaro suka yi masa.

“Jiya na sha samun kiraye-kirayen wayoyi daban-daban daga abokan arziki da ‘yan jarida, su na tambayar cewa jami’an tsaro sun gayyace ni.

“To na je kuma sun mutunta ni, a cikin girmamawa, mun tattauna kan batutuwan da suka shafi hanyoyin da za a daƙile hare-haren ‘yan bindiga, kamar yadda kowanen mu ke na sa bakin ƙoƙarin ta ɓangaren sa wajen ganin bayan wannan bala’i da ya addabi ƙasar nan. Amma dai babu wani abin fargaba, ko jayayya ko ɓacin rai a ɓangaren su. Sun mutunta ni, sun girmama ni.

A ranar Litinin ce kuma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya bayyana cewa Gumi bai fi ƙarfin doka ba, an riga an yi masa tambayoyi.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro suka yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, tambayoyi kan kalamansa na baya-bayan nan kan ‘yan bindiga a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a ranar Litinin.

A cewar ministan: “Gwamnati za ta yi komai don samun duk wani bayani da ake buƙata don magance matsalolin mu, jami’an tsaro suna nan suna aiki.

“Sheikh Gumi ko wasu mutane ba su fi ƙarfin doka ba. Idan yana da wasu shawarwari ƙwarara da suka dace kuma masu inganci da jami’an tsaro za su yi aiki da su, to za su ɗauka, amma idan suna tunanin shi ma yana yin wasu kalamai ne na ganganci, za a tsawata masa. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”

Idris ya ƙara cewa, “Bari in faɗa maku wani abu. Kuma ina sane da cewa jami’an tsaro sun gayyace shi don amsa tambayoyi.

“Idan ka yi wani kalami musamman kan tsaron ƙasar mu, ya zama wajibi jami’an tsaron ƙasar mu su yi ƙarin tunani kan hakan kuma suna yin haka. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”

People are also reading