Home Back

KIBIYAR AJALI: Direban tirelar da ya kashe mutum 14 a Masallacin Juma’a a Kano, Ya tsere

premiumtimesng.com 3 days ago
CORONAVIRUS: Jihar Abia ta maido lodin matasan Arewa da ta kama dankare cikin tirelan Shanu
Trailer full of People

Aƙalla mutum 14 suka mutu, yayin da wata motar tirela ta ƙwace ta afka cikin masu halartar Sallar Juma’a a Jihar Kano.

Ibtila’in ya faru a garin Imawa, kusa da garin Kura, kan titin Kano zuwa Zariya.

An ce tirelar mai lamba MKA 537 XN ta ƙwace wa direban, ta afka cikin masallatan.

An ce direban ya na kan hanyar Kaduna ne, yayin da yake ƙoƙarin ƙarasawa Kano, ya rage sauran kaɗan ya ƙarasa, hatsarin ya faru a garin Imawa, misalin ƙarfe 1:50 na rana.

Jami’an Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) daga Jihar Kano sun tabbatar da afkuwar mummunan hatsarin, kamar yadda Kwamandan Shiyya na Kano, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar, ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran hukumar, Abdullahi Labaran.

Ya an rufe mutum 9 da rana bayan tashi daga Sallar Juma’a, yayin da waɗanda suka ji raunuka kuma na can ana kula da su a asibiti a jihar.

Sai dai kuma jami’an tsaro sun tabbatar da cewa direban da tuƙa tirela ɗin ya tsere, ganin irin mummunar ta’asar da ya aikata.

People are also reading