Home Back

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf Ta Dauki Matakan Inganta Ilimi a Kano

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta dauki sabon mataki domin farfaɗo da darajar ilimi a jihar
  • Gwamna Abba ya ce bangaren ilimi yana buƙatar kulawa ta musamman a jihar Kano musamman abin da ya shafi malamai
  • Sabon matakin da gwamnatin jihar ta dauka ya biyo bayan dokar ta ɓaci da gwamnan ya saka a kan harkar ilimi ne a jiya Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, injiniya Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin samar da karin malamai da dakunan bincike a jihar.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin ganin ilimi ya inganta da kuma ganin jihar ta yi fice tsakanin sauran jihohin Najeriya.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf zai dauki malamai domin inganta ilimi. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa Asali: Facebook

Legit ta tabbatar lamarin ne cikin wani sako da mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin sadarwa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar ilimi a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da samuwar tarin matsaloli a harkar ilimi a jihar ciki har da ƙarancin kwararrun malamai.

Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa akwai ƙarancin samun horo akai-akai ga malamai da kuma rashin abubuwa na musamman kamar ruwa da banɗaki a makarantu.

Abba zai dauki malamai a Kano

Saboda rage matsalolin ilimi, gwamna Abba ya ce zai dauki malamai 10,000 da za a rika ba su horo domin ganin sun samu kwarewa kan aikin koyarwa.

Har ila yau ya kara da cewa za a dauki ma'aikata 1,000 a manyan makarantun jihar domin inganta ilimin gaba da sakandare.

Za a gina dakunan bincike a Kano

Wani karin mataki da gwamnan ya dauka shi ne cewa zai samar da ɗakunan bincike 300 a makarantu 100 da ke fadin jihar.

Ya ce hakan zai rika ba dalibai damar samun yin bincike mai zurfi da inganci da kuma kawo cigaba a jihar Kano da kasa baki daya.

A karshe gwamnan ya ce saboda rage cinkoson dalibai zai samar da karin ajijuwa 1000 a fadin jihar.

Yan adawa sun saka Abba a gaba

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya magantu kan irin kokarin 'yan adawa na kawo rudani a jihar a mulkin Abba Kabir.

Kwankwaso ya zargi jam’iyyun adawa da neman dagula jihar bayan kammala zaben inda suka shiga kotu domin kalubalantar zaben.

Asali: Legit.ng

People are also reading