Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Shekara Ɗayar Mulkin Tinubu: Aiki da aika-aika ba su shan inuwa ɗaya

premiumtimesng.com 2024/6/29
Ba za mu amince da juyin mulkin da Sojoji ke yi a Kasashen yammacin Afirka daga yanzu ba – Tinubu

Ranar Labara, 29 ga Mayu ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai cika shakara ɗaya kan mulki. Shekara ce wadda za ta sha nazari, sharhi da tuna-baya, bisa la’akari da irin alƙawurran da mai riƙe da irin wannan kujera ke ɗauka da kuma irin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

Auna nasarorin da aka samu a cikin wannan shekara ɗaya bisa ma’aunin ƙalubalen da ake fuskanta, abu ne bambarakwai.

Ita kan ta wannan gwamnatin ta karanci zukatan jama’a, kuma ta san abin da ke tsananin damun su, shi ya sa ta ce ba za yi ruguntsimin shagulgulan cikar shekara ɗaya kan mulki ba, sai dai a yi ‘sesa-sesa’ kawai.

Yayin da Tinubu ya cika shekara ɗaya, abin da zai fi zuwa cikin zukatan al’umma su ne, zafafan kalamai irin “tattalin man fetur ya tafi, ba cire shi”, sai faɗuwar darajar Naira, waɗanda su ne liman da ladanin da suka jefa tattalin arzikin Najeriya da ‘yan Najeriya cikin raɗaɗin tsadar rayuwar da ba a taɓa fuskantar tsadar kayan abinci da na masarufi kamar wannan shakara ba.

Tsadar rayuwa ta kanannaɗe ‘yan Najeriya, kuma a kullum sai yaɗo take ƙara yi cikin gidajen kowa da kowa, musamman talakawa da marasa galihu.

Matsalar tsaro da adalci wajen yin naɗe-naɗen muƙaman gwamnatin tarayya, rufa-rufa wajen gudanar da aikin gwamnati da bayar da kwangiloli, yin watsi ko rashin bin umarnin dokar tsarin mulki ta 1999, dukkan waɗannan ɓaranƙyanƙyamar sun kashe daraja da martabar ajandoji takwas na gwamnatin Tinubu, waɗanda aka raɗa wa suna ‘Renewed Hope Agenda’.

Za a iya yi wa Tinubu adalci cewa ya gaji tattalin arzikin da saura ƙiris ya rage ya durƙushe, wanda ya yi ta kururuwar cewa zai hau domin ya gyara, ko ya hau kuma zai gyara.

Misali, Buhari ya garargaje Naira tiriliyan 7.83 cikin shekaru takwas wajen biyan tallafin fetur.

Wannan ta sa an riƙa ji da ganin irin harƙallar maƙudan kuɗaɗen da aka riƙa yi a lokacin a NNPC, duk kuwa da cewa Buhari ne Ministan Fetur ba wani ba.

Saboda haka tabbas akwai aikin yin gagarimin gyaran tsaftace fannin a lokacin da Tinubu ya hau mulki. Hakan kuwa aka yi, ba tare da ɓata lokaci ba Tinubu ya cire tallafin fetur.

To amma ka inda Tinubu ya tafka kuskure, kamar yadda wasu ke cewa, gaggawar da ya yi wajen cire tallafin, ba tare da ya tuntuɓi ƙungiyoyin ƙwadago da masu ruwa da tsaki a harkar ba.

Sannan a lokacin da Tinubu ya cire tallafin fetur, ko ministoci bai kai ga naɗawa ba. Sai aka riƙa kame-kamen yadda za a fito da tsarin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwar da komai ya yi tsada sakamakon cire tallafin fetur. Shi ma tallafin ba wani abin a zo a gani ba ne.

Kuma wajen rabon kayan tallafin aka yi harƙallar da ta ci mai rabon tallafin, minista sukutum, wadda har yanzu a dakace ta ke. Aka bai wa gwamnonin jihohi ramcen Naira biliyan 2.5 kowane, domin ya samar da tallafin abinci. Amma duk lamarin bai canja zani ba.

Batun gaskiya maganar cire tallafin fetur ta zama ‘an ƙi cin biri, an ci dila’. Cikin watan Yuni 2023, an tara Naira tiriliyan 1.9, amma kuma tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba Naira biliyan 907. Cikin Afrilu 2024, an raba Naira tiriliyan 1.2.

Tinubu ya yi ƙoƙari ganin yadda a yanzu NNPC na kai kuɗi a CBN. Aikin binciken tonon sililin da Tinubu ya bai wa Jim Obazee abu ne mai kyau.

Sai dai kuma tulin basussukan da Tinubu ya ciwo duk da ya cire tallafin fetur, gyara ne, amma fa na gangar Abzinawa.

Gwamnatin Tinubu ta kinkimo aikin titin Naira tiriliyan 15, daga Legas zuwa Kalaba, mai tsawon kilomita 700, a lokacin da titina da yawa a faɗin ƙasar nan an yi watsi da su, sun lalace sai kashe fasinjoji suke yi.

Tallafin arzikin Naira a daburce ya ke, haraji ya yi yawa. Kwanan nan Aliko Ɗangote ya ce a duk Naira 100 da ya samu a siminti, gwamnati na ɗaukar Naira 54.

Shugaban kamfanin TotalEnergies, Patrick Pouyanne ya ce ya ƙi zuba jari na Dala biliyan 6 a Najeriya ya zuba su a Angola, saboda tsadar harajin Najeriya.

Har yau sai tsallen-baɗake da tsalle ɗaya ake yi kan ƙarin albashi. A cikin 2022 an yi hasashen mutum miliyan 133 ke fama da raɗaɗin talauci a Najeriya. A shekarar da ta gabata kamar yanzu ana sayar da litar fetur Naira 185, yanzu kuwa ta na Naira 750. Tsadar abinci kuwa ko daɗin ji babu. Haka tsadar haya da tsadar komai.

Ga matsalar tsaro, ga matsalolin komai. A irin wannan lokaci, ko da wani ya fito ya ce an samu ci gaba a cikin shekara ɗaya, to ɗan Najeriya cewa zai yi ci gaban mai ginin rijiya dai aka samu.

People are also reading