Home Back

Na Jajanta Wa Tinubu Kan Faduwar Da Ya Yi – Atiku

leadership.ng 2024/6/26
Na Jajanta Wa Tinubu Kan Faduwar Da Ya Yi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ya jajanta wa Bola Tinubu game da zamewar da ya yi lokacin hawa mota har ya fadi.

“Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da dan hatsarin da ya samu a lokaci da yake kokarin zagaya masu fareti a ranar dimokaradiyya. Ina fatan lafiyarsa kalau yanzu.”

A ‘yan kwanakin nan Atiku na ci gaba da sukar shugaba Tinubu kan wasu ayyukansa da jam’iyyar ta APC.

Ko a jiya Talata sai da jami’yyar PDP ta soki Tinubu, inda ta ce ‘yan Nijeriya a fusace suke kan irin manufofin da gwamnatinsa ke kaddamarwa.

A gefe guda kuma har yanzu babu wani martani daga gwamnati mai ci kan jajen da Atiku ya yi Tinubu.

People are also reading