Home Back

Ramadan: Saudiyya Ta Tuna da Kano, Ta Yi Mata Goma Na Arziki, Abba Ya Yi Godiya

legit.ng 2024/4/28
  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Saudiyya ta tuna da jihar Kano kan tallafin abinci ga marasa karfi
  • Gidauniyar Sarki Salman Ibn AbdulAziz ta ba da kayan abinci ga gidaje akalla 2,000 a kananan hukumomi takwas a jihar
  • Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yabawa Gidauniyar da wannan taimako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gidauniyar Sarkin Saudiyya, Salman Ibn AbdulAziz ta raba kayan abinci ga gidaje fiye da 2,000 a jihar Kano.

Gidauniyar ta raba kayan abincin ne musamman ga mutanen nasu bukata ta musamman a kananan hukumomi takwas da ke jihar.

Saudiyya ta gwangwaje 'yan jihar Kano da kayan tallafi saboda Ramadan
Gidauniyar Sarki Salman na Saudiyya ta raba kayan abinci a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Salman Ibn AbdulAziz. Asali: Facebook

Wane nau'in abinci aka raba a Kano?

Shugaban Gidauniyar, Abdulrahman Ibn AbdulAziz Al-Zaben ya ce sun yi hakan ne ga marasa karfi domin rage musu radadi a wannan wata na Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kayan da aka raba sun hada da kilo 25 na shinkafa da wake da kuma garri kilo hudu da sauran kayan abinci, cewar Daily Trust.

Wannan rabon abincin ya zo a dai-dai lokacin da ake cikin wani hali na matsin tattalin arziki a Najeriya.

Gwamnatin Kano ta yi godiya da tallafin

Yayin da ya ke jawabi, mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya godewa Gidauniyar da ta tuna da jihar a wannan yanayi.

Darakta-janar na hukumar NEMA, Zubaida Umar ta yabawa Gidauniyar kan wannan taimako da ta yi, Leadership ta tattaro.

Zubaidah wacce ta samu wakilcin daraktan ayyukan na musamman a hukumar NEMA, Fatima Kashim ta ce taimakon ya zo a dai-dai lokacin da ake buƙata.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ware biliyoyin kudi domin ciyar da mutane a watan Ramadan.

Dangote ya raba kayan abinci a Kano

A baya, mun ruwaito muku cewa Gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ta sanar da raba kayan abinci ga al'umma a jihar Kano.

Gidauniyar ta ce a kullum ta na ciyar da mutane 10,000 a wannan wata na Ramadan domin saukaka musu wahalar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

 
People are also reading