Home Back

Sakamakon farko na zaben Afirka ta Kudu

dw.com 2024/7/2
Hoto: RAJESH JANTILA/AFP

Kuri'un jin ra'ayin jama'a dai na ci gaba da nuna yiwuwar jam'iyyar ANC mai mulki na iya rasa rinjayen da ta ke rike da shi a karon farko cikin shekaru 30.. Da akalla kaso kasa da 20 da aka tattara ya zuwa yanzu, jam'iyyar ANC ta Shugaba Ramaphosa na da kashi 42%, akasin kashi 57 da ta samu a zaben 2019. Sannan jam'iyyar DA ta Democratic Alliance ke biye mata da 26%  sai wadda ta ke ta uku wato jam'iyyar EFF ta dan gwagwarmaya Julius Malema da kashi takwas yayin da ta hudu ke zama jam'iyyar tsohon Shugaba Jacob Zuma da ya kafa a baya-bayan nan mai kaso bakwai cikin 100.

Ba a dai sa ran samun sakamakon zaben kafin karshen wannan makon, kamar yadda hukumar zaben ke nunawa. Hakan kuma na nufin lallai ne jam'iyyar ta shiga hadaka da wata jam'iyya ko ma wasu kananan jam'iyyu kafin ta iya mulkar kasar. Jam'iyyar ta kafa shaidar zama a kan gaba a dukkanin zabukan da aka yi a kasar tun a shekara ta 1994, lokacin da marigayi jagoran gwagwarmayar kawo karshen mulkin wariyar launin fata Nelson Mandela ke jagorancinta.

Daga cikin abin da ya rage tagomashin jam'iyyar ta ANC dai har da karuwar rashin ayyukan yi tsakanin 'yan kasa da kuma aikata manyan laifuka a kusan kulli yaumin da yawan daukewar wutar lantarki sannan kuma uwa uba cin hanci da rashawa. Koda yake alamu na ci gaba da nuna damar jam'iyyar ta samu kuri'u mafi rinjaye, abin da zai bai wa shugaba mai ci Cyril Ramaphosa damar dorewa kan mulki.

Shugaban hukumar zaben Afirka ta Kudu Sy Mamabolo ya ce da wuya a yanzu a iya sanin sakamakon ganin ana lasafta kuri'u ne. Sai dai za mu iya cewa za a samu sakamako na sama da kashi 66 da aka gani a shekara ta 2019 Masu nazarin al'amura a kasar na cewa suna iya fitar da hasashe mai kyau da zarar aka samu sanin ko da akalla kashi biyar na adadin kuri'un da aka kada. Shi ma babban baturen zabe a yankin Midrand da ke birnin Johannesburg, ya ce masu zabe sun fito kusan fiye da abin da aka gani a shekarar 2019.

Tsohon shugaban kasar Thabo Mbeki, ya ce lokaci ne na sadaukar da kai ga kasa.

''Akwai bukatar mu hada kai a matsayin kasa, mu san gudunmawar da za mu bai wa Afirka ta Kudu, wannan abu ne mai matukar muhimmanci. Ya kamata mutane su fito a dama da su a wannan dandali na dimukuradiyya. Ya kamata ANC ta yi abin da ya dace na dawo da Afirka ta Kudu cikin hayyacinta''.

Sama da mutum miliyan 27 aka yi wa rajistar kada kuri'a a fadin kasar ta Afirka ta Kudu a wannan karon. A bisa doka dai hukumar zabe na da kwanaki bakwai ne ta sanar wa al'uma da sakamakon zabe bayan kammala shi, koda yake jami'an zaben sun ce za su bayyana sakamakon wannan karon ne a ranar Lahadin da ke tafe.))

People are also reading