Home Back

An Kaddamar Da Bikin Nune-nunen Shirye-shiryen Bidiyo Da Sinima Na Kasar Sin A Kasar Serbia

leadership.ng 2024/5/4
An Kaddamar Da Bikin Nune-nunen Shirye-shiryen Bidiyo Da Sinima Na Kasar Sin A Kasar Serbia

An kaddamar da bikin nune-nunen shirye-shiryen bidiyo da sinima na kasar Sin a birnin Belgrade, fadar mulkin kasar Serbia a yau, wanda babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da gidan rediyo da telebijin na kasar Serbia suka yi hadin gwiwa wajen gudanar da shi. Za a gabatar da shirye-shiryen bidiyo da sinima fiye da 10 da CMG ya dauka a kafar babban rediyo da telebijin ta kasar Serbia, wadanda za su shaidawa masu kallo na kasar, yanayin kasar Sin a sabon zamani, da bayani game da zumuntar dake tsakanin Sin da Serbia, da nuna kyakkyawar makoma a fannonin mu’amalar al’adu, da hadin gwiwa, da samun bunkasuwa tare, da kuma samun moriyar juna a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)

People are also reading