Home Back

Sojoji sun kashe ‘Yan ta’adda 121 sun kama wasu 253 a cikin mako guda a Najeriya

premiumtimesng.com 2024/5/2
GABA DAI SOJOJIN NAJERIYA: Yadda dakarun ‘Operation Haɗin Kai’ su ka murƙushen harin ‘yan ta’adda kan tubabbun Boko Haram

Hedikwatan tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 121, sun kamo wasu 253 sannan sun ceto mutum 244 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda a fadin kasar nan.

Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka a Abuja a karshen makon jiya.

Buba ya ce dakarun sun kwato bindigogi 223 da harsasai 2,756 inda a ciki akwai bindiga kirar M56- uku, AK-47- 115, PKT -3, bindiga kirar hannu – 24 da bindigar mafarauta -36.

Sauran sauran abubuwan da dakarun suka kama sun hada da bindiga kirar pistol -7, da Harsasai ma su yawa.

Bayan haka a Arewa maso Gabas rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan bindiga 52, sun kama wasu 137 sannan sun ceto mutum 78 da aka yi garkuwa da su a cikin makon jiya.

Dakarun sun Kuma kama makamai da suka hada da bindiga kirar M56-3, AK-47 40, PKT-3, bindiga kirar hannu -13, bam -2 da harsasai -889.

A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven da Whirl Stroke’ sun kashe mahara 47 sun kama wasu 17 Kuma sun ceto mutum 4 da aka yi garkuwa da su sannan sun kama makamai da dama.

A Arewa maso Yamma rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan ta’adda 62 sun kama wasu 12 sannan sun ceto mutum 162 da aka yi garkuwa da su.

Buba ya ce dakarun sun kwato bindigogi AK-47 -46, bindigogi kirar hannu -26,da harsasai da dama.

Ya ce rundunar sojin sama dake aiki a karkashin ‘Operation Hadarin Daji’ sun yi wa mabuyar ‘yan bindiga Maudi Maudi da Mallam Aibo dake karamar hukumar Safana a jihar Katsina ruwan bama-bamai.

“Rahotannin da rundunar sojin Najeriya ta samu ya nuna cewa dakarun sun kashe ‘yan ta’adda da dama a harin.

“Jami’an tsaron sun kuma kai a mabuyar maharan dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina inda a nan ma sun kashe mahara da dama.

Buba ya ce jami’an tsaro na ‘Operation Whirl Punch’ sun kama mahara 43 da makamai da dama.

Ya ce rundunar sojin sama ta yi wa sansanin mahara na Yadi da Abu Bilal dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna ruwan bama-bamai inda a nan ma sun kashe mahara da dama.

Daga nan Buba ya ce a Neja-Delta rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun kama lita 944,700 na bakin mai na sata, lita 171,060 na AGO da lita 1,500 na DPK.

Dakarun sun kuma ragargaza matatun mai 61, rijiyoyin mai 102, jirgin ruwa 41, tankunan mai 36 da dai sauransu.

People are also reading