Sanusi II vs Aminu: An Fara Zaman Ɗari Ɗari a Kano Bayan Hukuncin da Kotu Ta Yanke
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an fara zaman ɗari ɗari a Kano bayan hukuncin babbar kotun tarayya na ranar Alhamis kan dokar rusa masarautun jihar.
A zaman kotun na yau, Mai Shari'a Abdullahi Liman ya yi fatali da matakan da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka na tsige Aminu Bayero daga sarauta.
Jaridar TribuneOnline ta ruwaito cewa yanayin birnin na Kano ya sauya bayan kotun ta kuma tabbatar da cewa dokar da ta soke masarautun na nan daram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda rahoton ya nuna, an ga magoya bayan Sarkin Kano na 15, sun yi dafifi a gidan Sarkin na Nasarawa inda suke murnar hukuncin da kotun ta yanke.
Wani bidiyo da wani @tudunwada_mi ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna yadda dandazon jama'a ke maraba da Aminu Babba Dan-Agundi (Sarkin Dawaki Babba).
A wasu ɓangarori na jihar Kano kuwa, an ruwaito cewa mutane na taruwa gungu gungu suna tattaunawa kan hukuncin kotun da ya ba Aminu Bayero nasara.
Tun da fari, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke da zama a Kano ta tabbatar da dokar da ta rusa masarautu biyar na jihar wanda Abba Yusuf ya zartar.
Kotun ta kuma soke nadin da gwamnatin Kano ta yi Muhammadu Sanusi II matsayin sarkin Kano saboda ya biyo bayan umarnin farko da kotun ta bayar na dakatar da nadin.
Hukuncin dai ya haifar da wani nakasu a masarautar Kano, duk da cewa har yanzu Sanusi II ne sarkin Kano, amma za a ci gaba da fafata shari'a kan masarautar.
Asali: Legit.ng