Home Back

Da Ɗumi-ɗuminsa: Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Fara Binciken Gwamnatin el-Rufai

leadership.ng 2024/5/12
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata ta kafa kwamitin mutane 13 da zai binciki yadda aka gudanar da hada-hadar kudi, lamuni, bayar da tallafi da gudanar da ayyuka a karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-rufai.

Hon. Yusuf Mugu dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura ne ya gabatar da kudirin domin a binciki bayanan bashin da tsohon gwamnan ya karbo.

Kakakin majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya bukaci kwamitin da ya gayyaci duk masu ruwa da tsaki domin yi musu tambayoyi da kuma bincike kan lamarin.

Cikakken bayani Daga baya…

People are also reading