Home Back

Tottenham ta kammala ɗaukar Gray daga Leeds United

bbc.com 2024/10/6
Archie Gray

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta kammala ɗaukar Archie Gray daga Leeds United kan £30m ta kuma bayar da Joe Rodon kan yarjejeniyar £10m.

Gray ya saka hannu kan kwantiragin da zai kare a 2030.

Tottenham ta yi wa Brentford shigar sauri, wajen ɗaukar matashin mai shekara 18, wanda ya buga wa Leeds wasa 52 a dukkan karawa a kakar da ta wuce.

Tun farko Brentford ta fara auna koshin lafiyarsa, sai aka ji Tottenham ta biya ƙudin ƙunshin yarjejeniyarsa a ranar Lahadi.

Gray, wanda ya buga wa tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21, zai kuma iya yi wa Scotland wasa.

Rodon ɗan wasan tawagar Wales, wanda ke buga wasannin aro a Leeds United ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka hudu a ƙungiyar.

People are also reading