Home Back

Dillalan Mai Sun Fara Fargabar Farashin da Ɗangote Zai Sayar da Man Fetur a Najeriya

legit.ng 3 days ago
  • Dillalan mai sun fara hasashen da wuya a samu sauƙin da ake tsammani idan Ɗangote ya fara sayar da man fetur a Najeriya
  • Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Hammed Fashola ya buƙaci gwamnatin tarayya ta taimakawa Ɗangote ya riƙa samun ɗanyen mai a gida
  • Ya ce matuƙar za a bar attajirin ya sayo ɗanyen mai daga kasashen waje to zai wahala ƴan Najeriya su samu arhar da suke tsammani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nan da makonni biyu zuwa uku ake sa ran tataccen man fetur daga matatar attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Ɗangote zai shiga kasuwa.

Sai dai dillalan man fetur a Najeriya sun bayyana fargabar cewa man fetur na mamatar Ɗangote ka iya yin tsada fiye da yadda ake tsammani.

Matatar man Ɗangote.
Yan kasuwa sun fara fargabar farashin man fetur a matatar Dangote Hoto: Bloomberg/Contributor Asali: UGC

Ƴan kasuwar man sun faɗi haka ne duba da yadda kamfanonin mai na duniya suka hana matatar ɗanyen mai a nan cikin gida, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka matatar Dangote ta ci gaba da shigo da danyen mai daga kasar Amurka da wasu kasashe a farshi mai tsada.

Wannan dalilin da ya sa wasu dillalan ma su damu da sayen man dizal da man jirgin sama daga matatar ba saboda yanayin tsadar farashin.

Dillalan man sun shaidawa jaridar a ranar Litinin cewa farashin shigo da ɗanyen man daga ƙasashen waje zai iya yin tasiri ga farashin man fetur din da aka tace.

Bisa haka suka nuna damuwar cewa da yiwuwar farashin man fetur na matatar Ɗangote ba zai yi arha kamar yadda ake tunani ba.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce man fetur daga matatarsa zai shiga kasuwannin Najeriya a mako na uku a cikin watan Yuli.

'Yan kasuwa da 'yan Najeriya na fatan cewa matatar Dangote za ta rage farashin fetur wanda ya tashi daga N200 zuwa fiye da N600 bayan cire tallafin mai.

Da yake hira da ƴan jarida kan lamarin, mataimakin shugabn ƙungiyat dillalan mai masu zaman kansu (IPMAN) Hammed Fashola, ya ce shigo da ɗanyen mai daga waje zai iya tashin farashin man Ɗangote.

"Rashin samun ɗanyen mai a nan gida babban ƙalubale ne ga Ɗangote, shi kansa ya koka kan haka. Su kansu kamfanonin haƙar ɗanyen mai suna da na su dalilin, ba zai yiwu lokaci ɗaya su koma sayarwa Ɗangote shi kaɗai ba.

"Idan muna ci gaba da shigo da ɗanyen mai daga waje, ƙarin kashe kuɗi ne, matsala ce da muke tsoron za ta ƙara tsadar mai ba kamar idan a gida Najeriya aka saya ba," in ji shi.

Don warware wannan batu, shugaban na IPMAN ya roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa Dangote wajen samun danyen mai.

An yi gobara a matatar Ɗangote

A wani rahoton kuma wani bangare na matatar man Alhaji Aliko Dangote ya kama da wuta a jihar Lagos a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024.

Wutar ta tashi ne bangaren ETF da ke tace gurbataccen ruwan matatar inda aka tabbatar da kashe wutar da gaggawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading