Home Back

Za A Zuba Dala Miliyan 520 Don Habaka Noma A Jihohin Kudancin Nijeriya

leadership.ng 3 days ago
Barazanar Da Noman Masara Da Wake Ke Fuskanta A Nahiyar Afirka

Bankin Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka (ADB) da Bankin Raya Addinin Musulunci (IDB) da kuma Gidauniyar Habaka Aikin Noma ta Duniya (IFAD), na shirin fitar da dala miliyan 520; domin habaka aikin noma a jihohi shida na kudancin Nijeriya.

Za su fitar da kudaden ne, don yin aikin noma na musamman wanda ake kira da Zone (SAPZ).

Kwamishinan yada labarai na Jihar Kuros Ribas, Erasmus Ekpang ya bayyana cewa, Majalisar Zartarwar Jihar a zaman da ta yi karo na biyar, ta amince jihar ta fitar da kudin dauki da za a zuba a cikin wannan shiri na SAPZ; wanda wani aiki ne na gwamnatin tarayya.

Kazalika ya ce, sauran abokan hadaka na aikin kamar Bankin Raya Addinin Musulunci (IDB) da kuma Gidauniyar Habaka Aikin Noma na Kasa da Kasa (IFAD), za su bayar da dala miliyan 310, inda kuma gwamnatin tarayya za ta zuba dala miliyan 18.05 a cikin aikin.

Ya sanar da cewa, a cikin hadakar za a samar da ingantaccen Iri kamar na Masara, Alkama da kuma Farin Wake.

Gwamnna Jihar Sanata Bassey Otu, wanda a ofishinsa ne aka rattaba hannun yarjejeniyar a tsakanin kwamishin aikin noma na jihar da sauran masu hadakar, ya jaddada muhimmancin da aikin noman yake da shi, inda ya ce; shi ne babban fannin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai.

Kazalika ya sanar da cewa, daga cikin ayyukan aikin noma da gwamnatinsa ta kirkiro da su; wadanda suka hada da ‘Project GROW’, zai bai wa manoman jihar damar samun rance a kan lokaci tare da kara habaka aikin noma na jihar.

Shi ma a nasa jawabin, Daraktan Cibiyar Gudanar da Bincike na Tekun Chadi (LCRI), Alhaji Baba Gana Kabir ya sanar da cewa, jihar ta kafa tarihi a yankin kudu maso kudu a wannan fanni na aikin noma.

People are also reading