Home Back

ACF Ta Taso Tinubu a Gaba Kan Wahalar da Ake Fama da Ita a Najeriya, Ta Yi Gargadi

legit.ng 2024/6/18
  • Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta fito ta yi magana kan matsin tattalin arziƙi da wahalhalun da ƴan Najeriya ke fama da su a ƙasar nan
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu daga manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da su ne suka haddasa wahalhalun da ake fama da su
  • Ta yi gargaɗin cewa matsaloli masu ɗumbin yawa idan har mahukunta ba su yi gaggawar magance matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta nuna damuwa kan yadda wasu manufofin gwamnati mai ci ta Shugaba Bola Tinubu suka jefa ƴan Najeriya cikin wahala.

Ƙungiyar ta ACF ta ɗora alhakin taɓarɓarewar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da ake fama da su a ƙasar nan kan wasu manufofin da gwamnatin ta ɓullo da su a Najeriya.

ACF ta caccaki manufofin Tinubu
ACF ta ce wasu manufofin Tinubu ne suka jefa 'yan Najeriya cikin wuya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

ACF ta kuma yi gargaɗin cewa ƙasar nan na iya fuskantar matsaloli na zamantakewa, musamman a yankin Arewaci idan har ba a yi wani abu ba domin magance matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta ACF ta bayyana hakan ne bayan kammala taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da ta gudanar a birnin Kaduna ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

ACF ta soki manufofin Tinubu

Ta yi nuni da cewa talakawan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin wahala da ƙalubale, inda kullum suke fuskantar matsalar zaman kashe wando da hauhawar farashin kayayyaki.

Ta ƙara da cewa talakawan Najeriya na fama da saurin taɓarɓarewar rayuwa, tashe-tashen hankula, aikata ta’addanci da barazanar ƴan bindiga.

Kakakin ƙungiyar na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar wacce ya rattaɓawa hannu, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Me ya jawo taɓarɓarewar tattalin arziƙi?

Ƙungiyar ta ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙi a kan cire tallafin man fetur, da yawan harajin da gwamnatin tarayya ke ɓullowa da su.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Cike da damuwa NEC ta koka kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a yankuna uku waɗanda suka ƙunshi dukkanin jihohin Arewacin Najeriya.
"Kamar yadda ta saba faɗa, ACF na kira ga gwamnatoci a kowane matakai da su gaggauta shawo kan matsalar taɓarɓarewar yanayin rayuwar ƴan ƙasa."
"Ƙara sababbin haraji ya zama wani babban nauyi a wuyan ƴan Najeriya. Akwai buƙatar a samar da shirye-shirye waɗanda za su magance matsalar raguwar ƙarfin tattalin arziƙin ƴan ƙasa."

An soki salon mulkin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi magani kan kamun ludayin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Babachir Lawal ya bayyana cewa tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan karagar mulkin Najeriya ƙasar nan ta samu kanta cikin wani yanayi mara daɗi.

Asali: Legit.ng

People are also reading