Home Back

AJANTINAN DAI: Tawagar Messi sun Lashe Kofin Kudancin Amurka Karo na 16

premiumtimesng.com 2024/8/22
AJANTINAN DAI: Tawagar Messi sun Lashe Kofin Kudancin Amurka Karo na 16

Tawagar ƙasar Argentina ta samu nasarar lashe kofin kudancin Amirka na 2024 kuma karo na 16 a tarihi.

Ƙasar ta samu wannan nasarar ne, bayan doke tawagar kasar Columbia 1-0 a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Hard Rock dake birnin Miami a ƙasar Amirka.

Lautaro Martinez ne ya samu nasarar zurawa Argentina kwallo ɗayan, da ta bata wannan nasarar a mintina na 112, mintina bakwai kafin bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Lionel Messi ya fice daga wasan a mintina 66 da fafatawa, bayan raunin da ya samu a idon sawunsa.

Da wannan nasarar Argentina ta lashe manyan kofuna huɗu cikin shekaru huɗu a tarihin ta, inda ta lashe kofin duniya a 2022, Kofin Kudancin Amirka a 2021 da 2024 sai kuma Finalisima a 2022.

Bayan kammala wasan, an zaɓi ɗan wasan gaban Columbia James Rodriguez a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar, sai Emi Martinez a matsayin gwarzon mai tsaron raga, sai kuma Lautaro Martinez a matsayin ɗan wasan da yafi kowanne yawan zura ƙwallaye da guda shida.

Wasan ƙarshen nan, ya kasance na karshe ga Angel Dimaria, inda ya tabbatar da ajiye takalminsa ga ƙasar Argentina, amma zai ci gaba da bugawa Benfica kakar 2024/2025.

People are also reading