Home Back

Rikicin Siyasa Ya Ɓarke a Jam’iyyar Kwankwaso, NNPP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna

legit.ng 2024/7/5
  • Ana saura watanni uku a gudanar da zaben gwamnan Edo, jam'iyyar NNPP ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Fasto Ezena
  • A wata sanarwa da jam'iyyar, reshen gundumar ɗan takarar ta fitar, NNPP ta dakatar da Fasto Ezena saboda ayyukan zagon ƙasa
  • Sai dai ɗan takarar gwamnan ya ƙaryata wannan dakatarwar yana mai cewa aikin 'yan adawa ne wadanda ba halastattun 'yan jam'iyya ba ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Edo - Rahotanni sun bayyana cewa rikicin siyasa ya barƙe a jam'iyyar NNPP mai alamar kwando da kayan marmari ta Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ana saura watanni uku a gudanar da zaben gwamnan Edo, jam'iyyar NNPP ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Fasto Azemhe Azena.

NNPP ta dakatar da dan takarar gwamnan Edo
Dan takarar gwamnan Edo ya ki amincewa da korar da NNPP ta yi masa. Hoto: Legit.ng Asali: Original

Jam'iyyar NNPP reshen gunduma ta 10 a karamar hukumar Etsako ta Kudu ne suka dakatar da Fasto Ezena, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta dakatar da dan takarar gwamna

A yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumba, an ce an dakatar da Fasto Ezena saboda zargin yi wa NNPP zangon ƙasa, da ƙin mutunta tsare-tsaren ta.

Shugaban jam'iyyar na reshen gunduma ta 10, Kadiri Eshimokha; Sakataren jam'iyyar, Kwamred Imonikho Abdul; Shugabar mata, Misis Stella Afebua da shugaban matasa, Kwamred Eshiobo Johnson ne suka saka hannu a takardar dakatarwar.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa an miƙa takardar dakatarwar ga shugaban jam'iyyar na jiha, mataimakin jam'iyyar na ƙasa (shiyyar Kudu maso Kudu), da hukumar zaben jihar.

Dan takarar gwamna ya yi martani

Sai dai a wani martani da ya yi kan wannan dakatarwa, dan takarar gwamnan jihar ya ce wannan shirin wasu 'yan hassada ne kawai, waɗanda ba 'yayan jam'iyyar ba ne.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ɗan takarar gwamnan ya jaddada cewa shugaban jam'iyyar na gunduma ta 10 na asali, Goddy Iyamah ya ƙaryata dakatarwar.

"Mr Goddy Iyamah, ainihin shugaban jam'iyyar na gundumata ya ƙaryata wannan dakatarwa, kuma ya ce wadanda suka fitar da takardar ba 'yan jam'iyya ba ne."

- In ji Fasto Ezena.

Majalisa ta amince da nadin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da nade-naden Shugaba Bola Tinubu a hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta ƙasa (SEC).

Majalisar ta amince da nadin Emomotimi Agama a matsayin babban darakta na hukumar tare da kwamishinoni uku, mata biyu da namiji daya.

Asali: Legit.ng

People are also reading