Home Back

Gwamnatin Kano ta nemi ƴan sanda su fitar da Aminu Ado Bayero daga gidan sarki na Nassarawa

dalafmkano.com 2024/6/30

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nemi ƴan sanda su fitar da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, daga cikin gidan Sarki na Nassarawa, daga yanzu zuwa kowanne lokaci.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da yake gudanarwa yanzu haka a gidan gwamnatin jihar Kano, kamar yadda Dala FM ta rawaito.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya dake Gyaɗi-gyaɗi a Kano, ta yanke a yau, inda ta soke naɗin da gwamnatin Kano ta yiwa Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarkin Kano, amma ta ce dokar da majalisar dokokin jihar ta yiwa kwaskwarima na zata ce komai akai ba, kasancewar bata da hurumi akai.

Aminu Babba Ɗan Agundi ne dai ya yi ƙarar gwamnatin jihar Kano, da majalisar dokokin jihar yana ƙalubalantar rushe masarautun da tayi, lamarin da ya ce an tauye masa haƙƙi.

People are also reading